Wani mutum ya kashe kansa a Kano, yabar wasika mai sosa zuciya

 


Rahotan daga Kano na cewa wani mutum ya rataye kansa a garin tsamiya da ke Gezawa, tare da barin wasiƙar da ke tabbatar da cewa shi ya kashe kansa.

Wasikar dai na cewa "mutuwar tasa daga Allah ne dan haka ba wani ne ya aikata masa hakan ba".

Mutumin mai suna Babagana Usman mai shekaru 42 É—an asalin jahar Bornon ne da ke aure a tsamiya Babba, kuma ya rataye kansa a cikin É—akinsa.

Rundunarr yan sandan Kano ta bakin kakakinta, DSP Abdullahi Kiyawa, ta tabbatar da faruwar al'amarin, sannan tana kan bincike.

DSP Kiyawa ya ce rundunar su ta damu ganin cewa ana samun ƙaruwar mutanen da ke kashe kansu a Kano, don haka za su haɗa kai da malamai da sauran al'umma a bincikensu.

Ko a cikin kwanakin bayan sai da aka samu irin wannan labari na wani mutum a unguwar Sauna kawaji da wani matashi a unguwar masukwani da ke kano da suka kashe kansu ta irin wannan hanya


0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor