ALAMOMIN CIWON SANYIN

 


ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MAZA/ SANYIN GABA

Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i (STDs/STIs) .ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki. Alamomin ciwon sanyi ga maza sun sha banban tsakanin mutane wanda ciwon ya harba.

Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mutum - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar.

Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu, koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da cewa kau akwai cutar a jikin marar lafiyar. Maza da yawa na zargin suna da ciwon sanyi ne kaɗai a lokacinda suka ga wasu alamomi da basu saba gani ba (baƙi) ga al'aurarsu, misali , kamar: feshin ƙananan ƙuraje ko ƙaikayi, ko fitar farin ruwa, jin raɗaɗin zafi daga maraina da sauransu. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin maza zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar idan akwaita.

Ciwon sanyi anfi yaÉ—asa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu É—auke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaÉ—uwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba jima'i ba.

Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda rashin samun sahihin magani ko daÉ—ewarsa cikin jiki ba'a magance ba. Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai razana ciwon ba sai kaga yana ma mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru ba'a samu waraka ba.

Alamomin ciwon sanyin maza wanda akafi samu bainar mutane (game gari) :

1. ƙananan ƙuraje akan zakari, ko maraina ko ƙasansu.

2. ƙaikayi akan zakari (kan hular).

3. Fitar farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko É—orawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.

4. Jin zafi wajen yin fitsari.

5. Jin zafi yayin fitar maniyyi.

6. ƙuraje masu ɗurar ruwa da fashewa akan zakari.

Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba game gari ba:

1. Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.

2. Zafi da kumburin maraina

3. Zafi da kumburi daga kwararo da fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.

4. Zazzaɓi

Matsalolin jima'i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza:

1. RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci "Chlamydia" (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin Æ™arfin mazakuta idan ciwon yayi Æ™amari ba'a magance shi ba. Cutar maÉ“annaciya ce da take illa a É“oye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai É—auke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin Æ™arfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken Æ™arfin al’aurar namiji ko raguwar Æ™arfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin miÆ™ewar al’aura yayinda ake buÆ™atar fara jima’i.

Bugu da ƙari, matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin ƙarfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jinɗaɗin rayuwarsa ta jima'i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar bazai iya yima iyalinsa ciki ba saboda rashin miƙewar al'aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala, inshaaAllah.

2 RASHIN HAIFUWA:. Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , kamar dai ƙwayar cutar "Chlamydia", cutace daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, daga nan sai ya koma ɗorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda ɗan jini-jini. Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, ƙaikayin dubura, zubar jini, murar maƙoshi/maƙogwaro, jan- ido ko ƙananan kuraje, ciwon gaɓoɓi da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga namiji ko mace.

Nau'in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma kowanne iri akwai ƙwayar halittar dake haddasa ciwon da alamominsa da kuma matakan cutar a jikin 'dan adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/ƙanjamau (AIDS/HIV) tana daga cikin manyansu saboda itama anfi yaɗata ta jima'i, kuma sau dayawa itace ke gayyatar sauran cututtuka a jikin 'dan adam.

3) KANKANCEWAR ZAKARI, duk da dai cewa babu wani sahihin bayani a kimiyyance dake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma ƙarami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na ƙorafin cewa sanyi ya sace musu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan ƙanƙancewar alƙalummansu.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari, ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria), anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali, matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu. Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba, kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, da yardar Allah.

e) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi yana da haÉ—ari sosai. Ya zama dole ga mutane su tsaya ga matan su na Sunnah idan har suna son lafiyarsu. Ciwon sanyi yana nan akan hanyar mai neman mata da zinace-zinace, zai cimmasa. Akwai ciwuka masu haÉ—ari sosai kamar AIDS/HIV, wanda zasu iya wargaza iyali. Don haka maison zaman lafiyarsa da rayuwa mai kyau sai yaji tsoron Allah. Wanda kuma Allah Ya jarabta da ciwon bata hanyar zina ba to sai ya nemi magani, haka shima wanda ya tuba ga Allah. Allah Ya bawa Musulmi lafiya.

SAURIN INZALI /KAWOWA DA MAGANI

Biyan bukatar namiji da mace wajen jima'i yasha banban ta fuskar tsawon lokaci. Kashi 68 cikin 100 na mata suna bukatar minti 8 su biya bukatarsu da mazajensu, haka kuma, kashi 45 na wasu matan na bukatar minti 12 yayin saduwa. Abin mamaki shine, kashi 75 na maza na kasa jurewa su tsawaita lokacin biyan bukatarsu zuwa minti 3 ko 6, sabanin lokacinda wasu matan ke bukata don biyan bukatarsu.

Saurin inzali ko kawowa (Premature Ejaculation) yanayi ne da namiji yake saurin biyan bukatar jima'i da zaran zakari ya shiga farji cikin 'yan daƙiƙoƙi ko mintuna kaɗan koma kafin shigar zakari cikin farji kasancewar namijin baya iya tsawaita lokaci ko jure dadin jima'in da yake ji na tsawon wani lokaci, musamman saboda matsannanciyar sha'awa ko kamuwa da yawa. Saurin inzali na faruwa ba tare da mutum yayi wata niyyar yin hakan ba. Jima'i a wannan yanayi na karewa da zaran maniyyi ya fita daga jikin namiji. A wannan yanayi namijin baya iya yiwa sha'awarsa linzami ta fuskar rage sauri domin more jima'i na tsawon wani lokaci kuma baya iya gamsar da iyalinsa wacce saurin inzalisa ke hanata biyan bukatarta , ko haddasa rashin gamsuwarta. Kasancewar mata na bukatar lokaci mai tsayi fiye da na maza mafi yawan lokutta.

Shekaru da dabaru na yau da kullum saboda fahimtar jima'i tsawon lokaci a rayuwa nasa maza su fahimci yanda zasu magance matsalarsu da kansu ba tare da wani magani ba wani lokacin.

ABUBUWANDA KE HADDASA SAURIN INZALI / KAWOWA

Haryanzu dai babu wani sahihin bayani ko dalili dake bayyana dalilin saurin kawowa ba, saidai wasu bayanai akan dalilan da ka iya bada haske gameda matsalar saurin kawowa ga maza (premature ejaculation). Sune kamar haka:

1. Matsalar rashin karfin mazakuta (erectile dysfunction). Idan namiji baya da karfin gaba to akwai yiwuwar asami saurin kawowa lokacin jima'i , haka kuma, idan akwai karfin zakari to akwai yiwuwar dadewar yin jima'i mai tsawo tsakaninin ma'aurata biyu. Saboda haka, saurin inzali na iya zama wani lokacin alama ce ta rashin karfin zakari.

2. Yanayin halittar wasu mazajen. Wani haka Allah Ya halicce sa ko minti 1 baya iya yi da mace. Amma wannan baya nufin baza'a iya samun saukin yanayin ba. Za'a iya neman magani ko Allah Yasa a dace.

3. Samuwar hadari (accident) wanda zai iya shafar al'aurar mutum. Hadari wanda ya shafi lafiyar al'aura na iya haddasa matsalar saurin kawowa.

4. Magungunan kayan mata/da'a da mata keyi. Magunguna na matsi da mata ke sakawa cikin gaba domin matse/tsuke farji. Idan mace tayi amfani da wani magani gabanta ya tsuke/matse fiye da yanda maigidanta ya saba jinta zai iya sa maigidan yayi saurin kawowa saboda karuwar dadi ko dandanon jima'i.

5. Cututtuka masu shafar lafiyar jima'i, kamar cututtukan sanyin mara na maza da mata.

6. Ciwon damuwa ko fargaba na iya haddasa saurin inzali. Misali, idan mutum yayi sabuwar amarya budurwa ko bazawara , idan yana fargabar ko zai iya gamsar da ita ko damuwa akan wani abu, wannan tunani zai iya sanya saurin inzali a cikin saduwar su.

7. Yin istimina'i da gaggawa ( quick masturbation) da wasu matasa keyi kamin suyi aure, musamman yara don gudun kada a kamasu (wasa da al'aura ko zinar hannu). Yana shafar lafiyarsu, yana haddasa saurin kawowa lokacin jima'i.

8. Gado daga wajen mahaifan mutum (inherited traits). Akwai yiwuwar mutum yayi gadon saurin kawowa daga mahaifinsa ko kakansa ko wani jininsa, wato tsatstsonsa. Wato haka duk "family" nasu suke amma bai sani ba.

9. Matsananciyar sha'awar yin jima'i. Idan mutum ya kosa yayi jima'i , fitinar sha'awarsa ko kamuwa da yawa zata iya sanya shi yayi saurin kawowa da zaran zakarinsa ya shiga jikin mace ba tare da bata wani lokaci ba.

10. Rashin wasanni tsakanin ma'aurata kafin saduwa ta yanda macen zata iya fara biyan bukatar ta da wuri kafin maigida ya fara jima'i da ita ta gaba da gaba .

11. Sauyin abokiyar saduwa/ sabuwar amarya budurwa ko zawara. Yanayin sabuwar abokiyar rayuwa, wato sabuwar amarya ga maigida nada tasiri ga kwalwar namiji, yana sanya namiji ya rikice ko É—imauce da É—auki wanda hakan zai sanya shi saurin kawowa. Bugu da kari, Binciken ilimi na kiyimiyya ya nuna cewa samun sabuwar abokiyar saduwa (mata) na sanya maniyyin namiji inganci da kyau fiye da nada.

14. Canza salon kwanciyar aure, musamman mutum kada yayi kwanciya da iyalinsa wacce zata sa zakarinsa ya shige duka cikin gaban ta. Nutso (deep penetration) nasa saurin inzali.

13. Nau'in wasu magungunan. Akwai wasu magungunan da "side effects" nasu zai iya haddasa saurin kawowa ga mutum. Da sauransu, mu takaita haka.

MAGANCE MATSALAR SAURIN

KAWOWA

Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa , wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka , don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:

a) Rage ƙosawa/ƙagara. Mai saurin inzali ya kamata ya cire tunanin jima'i daga ƙwalwarsa a lokacinda yake saduwa da iyalinsa. Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafin fara jima'i zai iya sanya mutum "ya ƙone tun kafin ya tafasa". Masana sun nuna cewa bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima'i ba marar daɗi a lokacin saduwa na ƙarawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba. Ɗaukin jima'i baya biya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima'i ne yake aikatawa, ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima'i ne domin samun gamsuwa wacce iyalinsa da yake sha'awa take biya masa. Kamata yayi tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima'i ne domin ya biyawa iyalinsa bukata farko kamin tasa. Abin lura, ka ɗauka ma cewa ba jima'i bane kake yi a lokacinda kake tarawa da iyalinka.

b) A nemi kuɓewa ɗanya (okra) guda 5, a wanke sa'annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi ɗaya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa'annan a ɗaura akan wuta a rufe tukunya. Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tashe ruwan a kofin shayi , sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano , a bari ya huce kaɗan amma asha da ɗumi. Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka. Kubewa nada sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa ga maza.

c) A nemi citta (ginger) musamman ɗanya, a wanke a kuma karkare ta , sa'annan a dake ta , ayi shayi da ita , bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da ɗumi. Ayi hakan safe da rana. Citta nada sinadari mai zafi na "gingerol" mai sanya yawan gudanar jini ga laura , wanda hakan na sanya ƙarfin gaba da jinkirin kawowa.

d) A nemi man na'a-na'a (peppermint oil) mai kyau, musammman É—an Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan) . A wanke gaba da ruwan dumi , a goge lemar sa'annan a shafa man ga zakari ya shiga fata, ga kai (glans) da tsawon sandar zakari (shaft) , amma banda kofar fitsari (urethra). Musamman a shafa idan zakari yana mike, sai jira bayan minti 10 zuwa 15 sa'annan a sadu da iyali. Man na'a-na'a na rage "sensitivity" na zakari , wato rage kaifin É—anÉ—ano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima'i. Haka kuma za'a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na'a-na'a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfin gaba.

e) Fita daga gaban mace na 'yan mintoci a lokacinda mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/penis grip) a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.

f) Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu. Don haka idan mutum yana son ya daÉ—e bai yi inzali ba to ya tari jima'i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayi inzali.

g) Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist. Idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin É—aya daga cikin wadannan mutanen domin neman taimako. Akwai wasu hanyoyi da dama na magance matsalar saurin inzali.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor