MAGANIN TOILET INFECTION



Toilet infection cuta ce da mafi akasari ake daukanta a bandaki ko kuma ta hanyar jima'i.

Idan ba toilet infection aka fada ba wasu ba zasu fahimci me ake nufi ba. Kamar yadda kuka sani "Infection" dai kalmar turanci ce wacce a hausance ma'anarta take nufin kamuwa da wata cuta




To idan aka ce toilet infection ana nufin Ciwon da aka 'dauko a ban 'daki.




Shi wannan ciwon aka sarin yafi kamuwar mata masu zuwa kai tsaye a toilet su du'ka su biya bukatarsu ba tare da tunani akan cewa kafin fa in gabatarda bukata ta a bayin nan bari in fara zuba ruwa, domin ban san wace irin cuta ce take daddabe a wannan bayin ba.




To daga keyi wannan dukawar shikenan idan akwai irin wayannan bacteria's nan take zasu shiga cikin al'aurar taki su haifar miki wannan mugun ciwo. Ko kuma tanyar jima'i idan abokin zamaki yana dauke da wannan cutar, idan aka sadu akwai yiwur kamuwa da ita.




Daga cikin hanyoyin da wannan mugun ciwo ke samuwar mafiyawan mata itace, hanyar shiga ban 'daki ba'a wanke hannu da Sabulu ko kasa ba.




Irin wannan rashin wanke hannu da sabulu ko kasa yakansa hannun hagu yayi mu'amula da hannun dama daga kezo keci abinci ba tare da wanke hannu ba to fa shikenan wannan bacteria zata bi ta cikin bakin ki.




Wasa da hannu a cikin Al'aura (fingering) yana daga cikin manyan matsalolin da ke kawo shi, domin mai yiwuwa hannun na dauke da bacteria, daga ansa ka hannun kai tsaye mutum ya kai bacteriar ne da kansa.




Har wayau akwai Madigo (lesbian's) yana daga cikin abinda ke haifar da wannan matsalar domin akwai wata kankanuwar kwayar cuta (parasitic organism) idan har wadda ake madigo da ita na dauke da ita to nan take zata shafawa 'yar uwarta wannan cutar.




Zama da wando mai datti ko kuma ya kwana 2 a jiki shima yana haifarda wannan matsalar domin datti ko zufan mutum na iya 'daukar wayannan kwayoyin ya kaisu cikin al'aurar mace.




Haka ma saduwa da namiji mai 'dauke da kwayoyin parasitic organism kan sawa macce wannan matsalar.




MAGANIN WANNAN TOILET INFECTION

Dole ne a rika kula da tsaftace ban daki, ko da ban dakin tsaftatacce ne yana da kyau a kara kwarara ruwa domin su yi gaba da kowace karamar kwayar cuta da take wurin.




Dole ne a kula da cenja wando kullum tare da kaurace wa wando mai datti.




Idan har maccen da ke da wannan matsala tana da aure ya kamata su 'dan jin kirta gabatar da ibadar aure har ta gama shan magani, kuma yana da kyau asha maganin tare da miji.




Idan ana madigo ko wasa da hannu (Istimina'i) a daina yi.




A duk sa'adda aka shiga bayi a wanke hannu da sabulu haka ma idan za'a ci abinci.




Bayan duk anbi wayannan hanyoyin ga wani magani da za'a yi amfani da shi.




A nemi Garin Hulba Cokali 2 a rika dafawa da ruwa idan suka tafasa a tace a sha sau 2 a yini.




A nemin tafarnuwa Cokali 1 da Garin 'ya'yan Tafasa Cokali 2 da Garin 'ya'yan Zogala karamin Cokali 1 a saka a zuma kofi daya ana sha.




A nemi Sassaken mangwaro da Sassaken Bagaruwa a tafasasu idan sun rage zafi daidai yanda za'a iya zama arika zama cikin ruwan har tsawon kwana 14 (2weeks). In shaa Allahu idan aka bi wayannan hanyoyi za'a samu sauki wannan matsalar.




Muna fatan zaku tura wannan sakon ga 'yan uwa domin mu amfana mu duka

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor