Addu'ar maganin mantuwa

 


MAGANIN MANTUWAR KARATU

Assalamu Alaikum warahamatullahi

wabarakatuhu

malam inada wata babbar matsala

wacce na kasa gane maganinta shine

nikeso kataimaka min da maganin

wannan matsalar da take da muna.

Wannan matsalar itace,

" a duk lokacin dana karanta wani

abu ko kuma na saurara ko kuma

nikeso inyi wani dogon sharhi akan

wani abu sai inji kwakwalwata ta

kulle, sai na kasa yin abinda nikeso

inyi, haka kuma aduk lokacin da nike

makaranta bancika fahimtar abuba,

sannan inada yawan mantuwa malam

wani lokacin har abokaina suna

cemini banida fahimta idan muna

magana ".

Malam inaso a taimakamin da abinda

zai warkar da wannan matsalar tawa

domin ina samun qalubale da dama

acikin mutane da kuma makaranta.


AMSA

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi

wa barakatuhu.

Abi na farko da zakayi shine ka

Qaurace ma duk wani nau'in sa'bon

Allah. Domin kuwa rike karatu yana

daga cikin falalar Ubangiji. Ita kuwa

falalar Allah bata kebantar masu

sa'ba masa.

Abu na biyu ka zama mao yawan

neman kusanci da Allah ta hanyar

Kiyaye dokokinsa da yawaita

ambatonsa da kuma salati ga

Manzonsa (saww)..

Abu na uku shine ka yawaita Karatun

Alqur'ani domin shi kansa maganin

kaifafa Kwakwalwa ne.

Abu na hudu kuma duk lokacin da

zakayi karatu kayo Basmalah sannan

ka karanta wannan addu'ar sau uku :

"Allahumma innee astaudi'uka

jamee'a ma Aqra'uhu fee hadhal

Kitab. Hatta taruddahu fee waqti

Ihtiyaajee ilaihi, Innaka ala kulli

shay'in Qadeer".

Idan kuma Malami zai fara lekcha sai

kayi ma Annabi Salati (saww) sannan

kace : "Allahumma innee astaudi'uka

jamee'a ma Asma'uhu min Hadhal

Mu'allimi Hatta taruddahu fee waqti

Ihtiyaajee ilaihi". (sau uku).

Idan kayi wannan addu'ar kamar ka

bama Allah ajiyar abinda ka karanta

ko kuma kaji ne. Shi kuwa Allah in

dai an bashi ajiyar abu to ba ya

salwanta.

Abu na karshe kuma ka rika maida

hankalinka wajen kokarin fahimta da

kuma rike abinda ka fahimta. Kada ka

rika sanya wasanni acikin lamarin

karatunka.

Ka nemi Lubban Zakar kana zuba

cikin karamin cokali guda acikin

Shayin Na'a-Na'a kana shansa

kullum da safe. Shima Mujarrabi ne

wajen abinda ya shafi kaifafa basira

ko magance mantuwar karatu.

WALLAHU A'ALAM.


KARANTA:


Me karatu Don Allah kayi sharing zuwa group group, wannan sadaqatul jariya ce, ubangiji Allah yakai ladan kabarin iyayenmu Amen.


DAGA Net Age Blog


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

https://www.facebook.com/netage001/ 

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor