Mutane tara da aka yankewa hukuncin kisa a kano



Bayanan da BBC Hausa ta samu sun nuna 


 mutum tara aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya daga watan Janairu zuwa watan Agustan 2020.


Takardun kotuna daban-daban da BBC Hausa ta samu sun nuna cewa an yanke hukunce-hukunce kan mutanen ne bayan samunsu da hannu a aikata mabambanta laifuka.


An samu bakwai daga cikinsu da aikata kisan kai, mutum É—aya ya aikata fyaÉ—e yayin da aka kama É—aya da laifin É“atanci ga Annabi Muhammadu (SAW).


A makon jiya ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin sanya hannu kan takardar kashe Yahaya Sharif-Aminu, mutumin da aka samu da laifin batanci ga Annabi.

An yanke hukuncin farko ne ranar 11 ga watan Fabrairu, inda za a kashe Ali Abdullahi ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kisan kai.


Ga jerin mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan:

Ali Abdullahi



Kotu mai lamba Shida ta kama shi da laifin kisan kai inda ranar 11 ga watan Fabrairu aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Yakubu ÆŠalha


Shi ma Yakubu Kotu mai lamba Shida ce da ke birnin Kano ta kama shi da laifin kisan kai, kuma ranar 3 ga watan Maris ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Abdullahi Isyaku


Babbar Kotun Kano ta same shi da laifin kisan kai kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 16 ga watan Maris.

Mujahid Sa'id


Kotu mai lamba 13 ta same shi da laifin kisan kai inda a ranar 24 ga watan Maris ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Naziru Ya'u


Kotu mai lamba ÆŠaya ta same shi da laifin aikata kisan kai inda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 13 ga watan Yuli.

Shehu Ado Shehu


Kotu mai lamba Shida ce a Kano ta same shi da laifin kisan kai kuma a ranar 26 ga watan Yuni ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Isah Auta


Kotu ta mai lamba ÆŠaya ta yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan Isah Auta bayan ta kama shi da laifin kisan kai. An yanke masa hukuncin ne ranar 29 ga watan Yuni.

Yahaya Aminu


Babbar Kotun Shari'a ta jihar Kano ce ta same shi da laifin yin É“atanci da Annabi Muhammadu (SAW), inda ranar 10 ga watan Agusta ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mati Abdu


Shi ma Babbar Kotun Shari'a ta Kano ta kama shi da laifin fyaÉ—e kuma ranar 12 ga watan Agusta ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefewa.

Source: BBC Hausa

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor