Tarihin hamisu breaker

 



Tarihin Hamisu Breaker


Hamisu yakasance Mawakin hausa kuma jarumi Wanda yayi fice a fadin Nigeria musamman arewa dama nahiyar Africa gaba daya cikakken sunansa Hamisu Sa,id yusuf Amma anfisaninsa da hamisu breaker
Ya samu suna breaker ne tin yana dan rawa sabida irin kwarewarsa ake kiransa da breaker.


Haihuwar Hamish Breaker

Mawakin Ya kasance haifeffen garin Kano an haifeshi a 1992 a dorayi karamar hukumar kwale.

Mawakin yayi Primary da Secondary a dorayi amma haryanzu besamu damar cigaba da karatuba.


Daukakarsa Hamisu breaker

Breaker ya fara Waka tun yana makarantar islamiya yayi wakoki da dama kafin ya fara cire albums Mawakin yayi wasu finafinai kannywood kamarsu zainul abideel, sannan kuma yana hawa videon wakokinsa dakansa duk dacewa yakan baiwa Sauran jaruma kamarsu Kb international, Garzali miko, Mome Gombe dasauransu suhau wakar tasa.

Taurarinsa Sun fara haskawa a 2016 tinda ya fitar da wakar shimfidar fuska
Sannan ya Kara samun shahara da magoya baya tun bayan fidda Wakarsa ta jarumar mata Dayayi a shakarar 2020. Wakarsa ta jarumar mata tasamu karbuwa inda mutane sama da million suka kalleta. Wakar ta kasance tana daga cikin jerin wakokin da sukafi shahara cikin wakokin hausa.

KARANTA:


Hadaka

Mawakin yayi waka tareda mawakan da suka hada da Isah ayagi, namej, faruk m inuwa, lilin baba, Abdul katif da sauransu.


Karramawa

Wakar Jarumar Mata da ta ja hankali a arewacin Najeriya ta samu shiga fagen nazari a Jami’a, inda mashahurin malamin nazarin adabin baka Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau yayi dogon Bincike dakuma nazari kan yadda wakar tasamu karbuwa wajen al’umma.

Turn table chart ta wallafa cikin jerin wakokin ta na tantance wadanda suka fi shahara a YouTube inda ta hamisu breaker tazo na shida a wancan lokacin.

Kuma Hamisu yayiwa masoyansa alkawarin fidda wakar jarumin maza.



Matar Hamisu breaker

Kawo yanzu Mawakin baida mata kuma babu sahihin labarin wata budurwa da aka alakantasu ta shi
Albums

Mawakin yasake albums da dama da suka hada da :


-haseena
-Dalilin so da
-sone
-sakon amarya
-sirrin zuciya
-kalmar so
– bangaji ba dasauransu



Mabiya

Yanadaga  cikin mawakan da suke da dubbunan masiya a shafukansa na sada zumunta inda yakeda mabiya samada million a Instagram.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor