Yan bindiga sun sace daliban islamiya sama da dari biyu 200 a jihar neja



Rahotanni daga Jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya na cewa wasu 'yan bingida sun kai hari kan wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina inda suka sace dalibai da dama.


Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun sace gwamman dalibai makarantar Salihu Tanko Islamic School, koda yake sun saki wasu daga cikin daliban saboda kanana ne.

A cewar shaidun 'yan bindigar sun rika harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su dauke daliban.

Sai dai cikin wata sanarwa da gwamantin jihar ta fitar ta ce, an harbi mutum biyu lokacin harin kuma an tabbatar da mutuwar daya daga ciki, yayin da guda ke cikin mawuyacin hali.

Kazalika gwamnatin ta ce tana ci gaba da tattara bayanan tsaro kan harin, kafin daga bisani ta dauki matakan da suka dace.

Shugaban makarantar ya shaida wa BBC cewa akwai sama da dalibai 200 a cikin makarantar lokacin da yan bindigar suka shiga cikin harabar makarantar.

"Akwai dalibai da yawa a lokacin da suka zo sama da 200, amma wasu sun rika tserewa ta taga.

"Tabbas akwai sama da dalibai 100 da aka sace, amma daga baya sun rika koro yaran da ba su fi shekaru 4 zuwa 12 ba domin sun yi kankanta da yawa," in ji shugaban makarantar.

Ya kara da cewa da misalin yammacin ranar Lahadi ne 'yan bindigar suka shiga garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar ta Neja.

"A babura suka isa wajen dauke da bindigogi, babu wanda ba a firgita ba a garin, tunda harbe-harbe kawai suke yi ta ko ina," a cewarsa.

Sace daliban makaranta a Najeriya na neman zama ruwan dare, ko a watan Fabirairu sai da aka sace É—aliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda 41 a Jihar.

Source: BBC Hausa

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor