Abubuwan da shugaban Najeriya BUHARI zai yi a ziyararsa ta Borno



Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
zai kai ziyara jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da gwamnan jihar Borno ya fitar mai sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Isa Gusau.

Borno ce jihar da ta zama hedikwatar ƙungiyar Boko Haram inda ake fama da hare-haren mayaƙan.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya roƙi ƴan jihar da su ba da goyon baya da fatan alheri a yayin ziyarar.

"Ina sake gode muku kan goyon bayan da kuka bai wa gwamnatin nan. Ina godiya bga kowa da kowa, kan goyon bayanku da fatan alherinku da addu'o'i da kuma zamantowarku ƴan ƙasa na gari," kamar yadda sanarwar ta ce.

Lokaci na ƙarshe da Shugaba Buhari ya kai ziyara Borno shi ne ranar 12 ga watan Fabrairun 2020, inda har wani dandazon mutane suka yi wa shugaban ihun ''ba ma yi, ba ma yi''.

  • Daga cikin dalilan ziyarar Shugaba Buhari Borno a wannan karon kamar yadda gwamnatin jihar ta faÉ—a akwai:Shugaba Buhari zai kai ziyarar ne don duba yanayin tsaron da yankin arewa maso gabas É—in ke ciki.
  • Sannan zai Æ™addamar da wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ta aiwatar
  • Shugaban zai kuma Æ™addamar da rukunin farko na gidaje 10,000 waÉ—anda ya amince da gina su tare da samar da kuÉ—aÉ—en yin su, don sake tsugunar da Æ´an gudun hijira.

"Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Buhari ta kamma gina gidaje 4,000 cikin 10,000 da aka amince a gina wa ƴan gudun hijira.

"Wasu daga cikin gidajen nan suna yankin Kaleri da Dalori da sauran wurare," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara jaddada gamsuwarta kan yadda "gwamnatin Buhari ta shawo kan matsalar tsaron sosai, ba kamar yadda abin yake a baya ba."

"Gina waɗannan gidaje ya ta'allaƙa ne ga samun zaman lafiyar da aka yi a yankunan jihar Borno.

"Na san har yanzu muna fama da matsalar tsaro, amma kuma idan muka waiwaya baya za mu ga cewa an samu sauƙi musamman a yadda a baya wasu yankunan ma ba a shigarsu," in ji sanarwar.

Sai dai duk da wannan yabo da gwamnatin jihar Borno ta yi wa gwamnatin Buhari, masu sharhi na ganin da sauran rina a kaba sosai a yaƙin da ake a ƙoƙarin daƙile ƙungiyar Boko Haram.

Source: BBC hausa

Join Our Telegram Channel for More Insights.  JOIN NOW

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor