Gwamnatin kano ta dakatar da mijin aljana sayar da magungunan gargajiya



Gwamnatin jihar Kano ta sanya wa mutumin da ya yi ikirarin cewa shi mijin aljana ne takunkumi na sayar da magungunan damfara ga al'umma.


Kwamishinan harkokin addini na jihar Muhammad Tahar wanda aka fi sani da Baba Impossible ne ya sanar wa BBC Hausa hakan bayan kammala taron muƙabala da mutumin.


A kwanakin baya ne wasu kafafen yaÉ—a labarai suka ruwaito cewa Malam Ahmad Ali Kofar Na'isa ya yi ikirarin cewa tun yana yaro ya faÉ—a a rijiya aljanu suka É—auke shi suka mayar da shi Masar tsawon shekara shida.


Ya kuma ce daga bisani sun mayar da shi wajen mahaifiyarsa, sannan a yanzu yana auren aljana har suna da Æ´aÆ´a uku.


Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce ƙwarai da gaske a tsakanin mutane inda ya zama abin al'ajabi ga wasu yayin da wasu kuma ya ba su taƙaici.


Baba Impossible ya ce cikin sharuÉ—É—an da aka gindaya wa Mijin Aljana har da hana shi tara mutane mata da maza a gidansa kamar yadda yake yi.


Sannan an hana shi magana da 'yan jarida, kuma rumfar ƙofar gidansa da ake taruwa an sa mai unguwar yankin ya cire.


"Duk wani abin da zai kawo tartsatsi an hana shi yi har sai abin da gwamnati ta ce," a cewar Baba Impossible.


Ya ƙara da cewa: "Ita gwamnati kullum abin da take kallo shi ne abin da ya shafi al'umma, ba ta son abin da zai kawo tashin hankali kuma ba ta son abin da al'umma za ta cutu ta yadda za a dinga cutar da mutane ta wata hanya.


A wata hira da ya yi da ƴan jarida a ranar Litinin da aka yi muƙabalar, Malam Ali ya ce ya saki aljanar matarsa saki uku ras, sannan ya ƙaryata duk abubuwan da ya dinga cewa sun faru da shi a baya, tare da ƙaryata kansa kan duk abin da ya ce yana yi.


Kwamishinan harkokin addinin ya ce tun farkon samun labarin Malam Ali Kofar Na'isa sai gwamnati ta aika wa Sarkin Kano cewa a nemo shi, inda aka tura masu unguwannin da mutumin ke zama don nemo shi don yin muƙabala.


"Sannan aka kawo jami'an tsaron farin kaya da masu kaki, aka zo aka hadu aka tattauna. Muka kira shi muka sa masa abin da aka gani, inda yake cewa ya fada a rijiya ne aljanu suka raine shi shekara shida suka dawowa da uwarsa.


"Kuma ya auri aljana sun haifi ƴaƴa uku, da sauran ƙarerayi har da batun cewa yana yin kuɗi. Daga ƙarshe sai ya ce duk ƙarya yake yi waɗannan abubuwan ba su faru ba.


"Sai muka ce me ya sa ya yi hakan? Sai ya ce ya yi ne saboda iyali sun masa yawa, ƴaƴansa 11 kuma yana so ya samu kudin abinci kuma mutane ba sa karɓar abu na gaskiya idan ka zo musu da magani, shi ya sa ya yi haka.


"Muka ce to kudaden fa da yake yi na damfara? Sai ya ce ya yarda wannan ma ba daidai ba ne a yi haƙuri," kamar yadda Baba Impossible ya bayyana.


Kwamishinan ya ce an dakatar da Mijin Aljana daga yin waɗannan ƙarerayi a gwamnatance.


"Ba a hana shi sayar da magunguna ba in dai na gaskiya ne, amma duk wani abu na damfara da yaudara an hana shi," in ji shi.


Sai dai wasu na ganin an tursasa wa Malam Ali ne ya ƙaryata kansa, amma Baba Impossible ya ce "wanda duk ya ce an tursasa masa sai ya kawo hujjar hakan, tun da mu ai ba jami'an tsaro ba ne.


"Kiransa muka yi muka zo da hujjoji daga littatafan addini muka zube masa muka ce ya zo da mutum É—aya da ya auri aljana a tarihin Musulunci, amma ya kasa.


"Ya yarda ƙarya yake yi sannan ya ce ba zai sake ba," in ji Kwamishina.


Baba Impossible wanda ya sha yin rubuce-rubuce tsakanin sosai kan batun mu'amalar mutum da aljan ya ce akwai bambancin jinsi tsakanin mutum da aljan.


Ya ce duk wata hulɗa tsakanin mutum da aljani ƙarya ce. "Aljani bai san gaibu ba. Duk mai neman magani ya je ya nemi sahihi kawai.


"Aljani ba shi da tasiri, mutum ya fi aljani daraja. Mala'ika ya fi mutum shi kuma mutum ya fi aljani, haka abin yake," in ji shi.


Ya ƙara da cewa daga yanzu gwamnati za ta faɗaɗa sa ido a kansu su daina yaudarar mutane. "Idan magani na gaske ne ba sai an hada da karya ba, ba za mu bar hakan ta ci gaba da faruwa ba.


"Ba za mu yarda ba, gwamnati za ta tattaro irin wadannan mutane ta hana su. Idan sun ƙi za mu kai su gaban shari'a.


"Don haka ba za mu bari a zo da wata maganar aljani ana ruɗar mutane ba.," kamar yadda ya ƙara da cewa.


Kwamishinan ya ce za su rubutawa gwamnati rahoto kuma za su saurari abin da za ta ce, idan gwamnati ta ce a bar magana ta wuce tun da ya ba da haƙuri to shi kenan, idan kuwa ta ce a gabatar da shi a kotu to jami'an tsaro zasu karɓi ragamar.

Source: BBC hausa

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor