Police sun hallaka yan bindiga biyar imo state



'Yan sandan jihr Imo sun ce sun dakile wani hari da 'yan bindiga sulka kai hedikwatar 'yan sanda ta jihar a ranar Lahadi, tare da kashe mutum biyar daga cikin maharan.

Wannan ne karo na biyu da ake kai wa hedikwatar 'yan sanda da ke Owerri hari tun lokacin da aka fara kai hare-hare kan jami'an tsaro a yankin kudancin Najeriya.

A ranar 5 ga watan Afrilu, wasu 'yan bingida da ake zargin 'yan IPOB ne suka kai wa hedikwatar hari da kuma kai hari gidan yarin jihar tare da sakin firsunoni 1844,

Kakakin 'yan sanda na jihar SP Bala Elkana cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce maharan sun kutsa cikin ginin ofishin ne da safiyar ranar Lahadi amma sun tara da jami'an da ke aiki a lokacin da suka nuna musu turjiya.

"Sun yi kokarin samun damar shiga cikin harabar hedikwatar ta wani wuri da ke kusa da ginin, amma an dakile harin nasu.

"Sun je wurin ne a wata farar bas kirar Hummer, an kashe biyar daga cikinsu yayin musayar wuta wasu kuma sun tsere da raunuka jikinsu.

"Mun kwace motar da suka je da ita da kuma bindiga kirar AK47 guda hudu," kamar yadda sanarwar da bayyana.

Source: BBC hausa

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor