Saudiya ta bada dama mata suyi aikin hajji ba tare da muharrami ba



Ma'aikatar kula da aikin Hajji a Saudiyya ta sanar da cewa mata za su iya yin rijistar aikin Hajji ba tare da muharrami ba.

Sanarwar ta ce mata za su iya zuwa da kansu su yi rijistar aikin Hajjin bana ba tare da namiji muharraminsu ba.

Kuma an ƙayyade shekarun matan da za su yi aikin Hajji daga shekara 18 zuwa 65 waɗanda kuma aka yi wa rigakafin korona.

A ranar Asabar ne hukumomin Saudiyya suka taƙaita yawan musulman da za su yi aikin Hajji. Ƴan ƙasar Saudiyya ne kawai za su gudanar da Hajjin bana saboda annobar korona.

A ranar Lahadi ne kuma aka soma rijistar masu niyyar aikin Hajjin kuma za a ci gaba har zuwa 23 ga wata.

Source: BBC hausa

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor