Wata Mata ta haifi ƴan 10 a Afirka Ta Kudu

 


Wata mata ƴar Afirka Ta Kudu ta haifi ƴan 10 a wani al'amari da bai taɓa faruwa ba a duniya.


Mijin Gosiame Thamara Sithole ya ce sun sha mamaki ƙwarai da haihuwar ƴan goman bayan da hoton cikin da aka yi mata ya nuna cewa ƴan takwas za ta haifa.


Bayan saukar matar a ranar Litinin da daddare, mMijinta Teboho Tsotetsi ya shaida wa kafar yaɗa labaran Pretoria News "ta haifi maza bakwai mata uku.


Ms Sithole, mai shekara 37, a baya ta haifi ƴan biyu, waɗanda a yanzu shekarunsu shida.


An ce mai jegon na cikin ƙoshin lafiya bayan da aka yi mata tiyata lokacin da cikin ya cika mako 29, a birnin Pretoria a ranar Litinin da yamma.


Wani jami'in Afirka Ta Kudu ya tabbatar wa BBC batun haihuwar, amma wani jami'in ya ce har yanzu ba su ga jariran ba.


Kundin Tarihi na Guinness World Records ya shaida wa BBC cewa yana bincike kan lamarin Ms Sithole.


A yanzu wata mata ƴar Amurka ce ke riƙe da kambun Guinness World Record bayan da ta haifi ƴan takwas a shekarar 2009, kuma duk suka rayu.


A watan da ya gabata ma wata mata mai shekara 25 Halima Cissé daga Mali ta haifi ƴan tara, waɗanda rahotanni suka ce suna cikin ƙoshin lafiya a wani asibiti a Moroko.


Yawanci cikin ƴaƴa da yawa kan zube ne ko a haife su babu rai, a cewar wakiliyar BBC kan harkar lafiya Rhoda Odhiambo.


Ba a faye haihuwar jarirai masu yawa a lokaci guda ba, kuma yawanci a kan samu irin hakan ne a dalilin fasahar inganta ƙwayayen haihuwa - amma a wannan lamarin ma'auratan sun ce ba su yi wani abu na inganta ƙwayayen haihuwa ba, ikon A;lah ne Ya sa suka samu ƴan goman.

Addu'o'i da rashin barci


Da take hira da kafar Pretoria News wata ɗaya da ya gabata, Ms Sithole ta ce rainon cikin ya ba ta wahala a farko-farko kuma ta yi ta yin addu'ar haihuwa lafiya, tare da rashin samun isasshen barci don damuwar me zai faru.


"Ta yaya za su iya zama a cikin mahaifa? Za su rayu?" tambayoyin da take yi wa kanta kenan, amma likitoci sun ba ta tabbacin cewa mahaifarta na ƙara girma.


A lokacin da ake tunanin ƴan takwas ne a cikin nata, Ms Sithole ta yi ta fama da ciwon ƙafa kuma likitoci sun gano cewa biyu daga cikin jariran takwas sun shiga wani waje ne da ba na zamansu ba.


"An gyara wannan matsalar kuma tun lokacin sai na samu lafiya. Na ƙagu na ga ƴaƴana," kamar yadda ta cewa wata jarida a lokacin.


Mijinta ma ya ce jin sa yake tamkar a duniyar wata, kuma yana jin kamar yana ɗaya daga "cikin nagartattun bayin da Allah Ya zaɓa. Mu'ujiza ce da na ji daɗinta sosai."


Sau biyu aka haifi ƴan tara a duniya waɗana aka sani - amma dukkan jariran ba su yi tsaon rai ba, kwanaki kaɗan kawai suka yi suka rasu.

Source: BBC hausa

1/Post a Comment/Comments

Post a Comment

Previous Post Next Post

header

Sponsor