MAGANIN BASUR KOWANNE IRI



MAGANIN BASUR KOWANNE IRI


Idan an riga an kamu da ciwon basur kuma sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi:-

.

★ A samu lemon-tsami guda uku, tsohuwar-tsamiya guda uku, jan-gauta guda uku, barkono guda biyar, sabulun sha kamar girman lemon tsami.




In aka tashi sai a hade su wajedaya, a jika, su kwana. Kullum sai a tsiyayi rabin kofi a sha da safe kafin a ci abinci. Ana diba ana kara ruwa, har sai ya salamce sannan a zubar.




Wannan magani ne na Basur sosai. Indai ka hada shi zai warke, ka rabu da shi da iznin Allah.

.

.

★ A samu madacin qasa daidai misali, a wanke shi, a zuba a cikin tukunya. A zuba ruwa da jar kanwa kadan, a dora akan wuta.




Idan ya huce, sai a dinga shan rabin kofi kullum sau uku. Da safe rabin kofi, da rana rabin kofi da daddare ma rabin kofi.

A dinga sha kullum ana kara ruwa har ya salamce. A cigaba da hadawa har sai an warke sarai.

.

★ A samu sassaqen itacen mangwaro, da sassaqen kadanya, da sassaqen dorawa, da sassaqen madaci amma madacin kadan ake bukata.




Sai a hade su wajedaya a wanke a zuba jar kanwa kadan.




A tafasa, kullum a sha rabin kofi sau uku kafin a ci abinci.




Idan kuma basur din mai tsiro ne ko wanda ake fitar baya, to idan an tashi sai a tafasa magungunan a zuba ruwan a cikin babban mazubi. Sai ka tsuguna, tururin ya dinga shiga karkashinka, idan ya dan huce kuma sai a shiga ciki a zauna tsawon yan mintuna ko kuma a dinga kama ruwa da shi.




Insha Allahu indai an hada wannan ana sha ana shiga ciki, to lokaci kadan za a rabu da basur kowane iri ne.

.

★A samu 6awon dorawa, a hada da jar kanwa a tafasa. Sai a dinga tsugunawa yadda tururin zai dinga shiga cikinka sosai, idan ya dan huce sai a shiga ciki a zauna ko a dinga kama ruwa da shi. Sannan a dinga tsiyaya ana sha. Shi ma hanya ce ingantacciya ta maganin basur.

.

.

★ A samu man habbatussaudaa da man tafarnuwa da man zaitun. Sai a hada su waje daya. Sai ka samu auduga mai kyau ka dangwali wannan man kay matsi da shi a karkashinka, musamman in za ka kwanta da daddare. Kullum ka dinga yin haka sau daya. Wannan yana saurin kashe basur mai tsiro da maganin tsatstsagewar dubura.


KARANTA:

★A samu garin sanamakiy da zuma. Sai a tafasa garin rabin cokali, a sa zuma daidai gwargwado. Sai a sha kullum sau daya.




Yana maganin kashin jini, da taurin bayan gida, yana fitar da dattin cikin cikin kankanin lokaci. Saidai wannan banda mace mai ciki, banda yara kanana.




★A samu `ya`yan raidore da kumfar maliya da garin bagaruwa, sai a hada su waje daya a tafasa. Sai ya tsuguna tururin ya dinga shiga jikinsa, idan ya dan huce sai ya zauna a ciki ko kuma ya dinga kama ruwa da shi. Wannan yana kone tsuron basur yana maganin tsatstsagewar dubura kuma yanay wa mata maganin sanyi wato infection.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor