MAGANIN CIWON MARA



Maganin ciwon Mara da yardar Allah.




Na zabi n sake posting wannan maganin ne duba d yanda "yan'uwa musamman mata su ke t kiraye kirayen n sake posting din sa kasancewar matsalar su tapi shafa a rayuwa shi yasa n sake maimaita shi saboda mahimmancin sa gare su.




HANYA TA DAYA:

A samu tafarnuwa da nonon tinkiya da man Shanu da Zuma sai a hadasu, idan suka hade sai a rika shafawa a marar.

Za a samu sauki da Izinin Allah.




HANYA TA BIYU:

A samu garin Zi'itir (Si'itir) kamar cokali biyar a hada da Zuma a motsa sai a rika shafawa a wajen da yake ciwon.

Za a samu waraka da yardar Allah.




HANYA TA UKU:

A samu garin Hulbah a tafasa a rika sha in shaaAllah za a samu sauki.




HANYA TA HUDU:

A samu man Habbatussaudā' da man Zaitun da Jan turaren Miski, in da halo a hada da garin Hiltit (Hantiti) a hada su waje guda sai a rika shafawa. Za a samu sauki da Izinin Mahaliccin mu (Shi ne Allah)



KARIN BAYANI;



Shi wannan hadin na hudu ba wai sai lallai ciwon Mara ba, a'a duk inda yakewa mutum ciwo da zarar ya shafa shi zai samu sauki da yardar Allah. Zaiji kamar an dauke masa ciwon.




Ina rokon Allah da sunayen Sa Yā Hayyu Yā Qayyum yabawa kowa lpy.

FUKANMU NA SADA ZUMUNTA 
https://www.facebook.com/netage001/

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor