Addu'oi da zikiri a musulunci


  ADDU'O'IN TASHI DAGA BARCI

"Alhamdu lillaahil-lazi ahyaana ba'ada maa amaatana wa ilaihin nushuuru". 

(Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauki rayukanmu, kuma zuwa gare she tashi yake).

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:wanda ya farka da daddare ya ce:

"Laa'ilaaha illallaahuu wahdahuu laa shariikalahuu lahul mulku walahul hamdu,  wahuwa ala kulli shai'in kadiiruun. Subhaanallaahi wal hamdu lillahi walaa ilaaha illallahu Allahu akbaru walaa haulaa wala kuwwata illaa billaahil aliiyil aziimi, Rabbigfirlii". (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai,  babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne,  kuma Shi Mai iko ne akan  komai. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara Abu karfi sai gurin Allah, madaukaki, mai girma. Ya Ubangijina! Ka gafarta mini).


"Inna fii khalkis-samaawati wal ardhi waktilaafil laili wannahaari la ayaatul li ulil albaab. Allaziina yazkurrunaallaaha kiyaaman wa ku'uudan wa alaa junuubihim wayata-fakkaruuna fii khalkis-samaawatil wal ardhi rabbana maa khalakta hazaa baadilan subhaanaka fakinaa azaaban naari. Rabbanaa innaka man tudkhilun naara fakad akhzaitahu wamaa liz zaalimiina min ansaar. Rabbana innanaa sami'ina munaadiyan yunadii lil imaani an aminuu bi rabbikum fa'aamannaa rabbanaa fagfir lanaa zunubanaa wa kaffir anaa sayyi'atinaa watawaffanaa ma'al abraar. Rabbana wa atinaa maa wa'adtanaa alaa rusulika walaa tukhzina yaumal kiyaamati innaka laa tukliful mii'aada. Fastajaaba lahum rabbuhum annii laa udhii'u amala aamilin minkum min zakarin au unsaa ba'adhukum min ba'adhin fallaziina haajaruu wa ukhrijuu min diyaarihim wa uuzuu fii sabili wakaataluu wa kutiluu la'ukaffiranna anhum sayyi'atihim wala udkhilannahum jannatin tajri min tahtihal anhaaru sawaaban min indillahi wallahu indahu husnussawab. Laa yagurrannaka takallubul laziina kafaruu fil bilaadi mataa'un kaliilun summa ma'awaahum jahannamu wa bi'isal mihaadu. Laakinillazinat takau rabbahum lahum jannatun tajri min tahtihal anhaaru khaalidiina fiihaa nuzulan min indillahi wama indillahi khairun lil abraar. Wa inna min ahlil kitaabi laman yuuminu bil laahi wamaa unzila ilaikum wamaa unzila ilaihim khaashi'iina lillaahi la yashtaruuna bi ayaatillaahi samanan kalilan ulaa'ika lahum ajruhum inda rabbihim innal laaha sari'ul ilhisabi. Ya ayyuhal laziina aamanus birru wa saabiruu wa raabiduu wattakullaha la'allakum tuflihuuna. (Al-imrana, aya ta 190 zuwa karshen surar). 

(Hakika a cikin halittar sammai da kassai, da sabawar dare da rana, lallai akwai ayoye ga ma'abota hankula. (Su ne) wadanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma a zaune da kuma a kishingide, suke kuma tunani a kan halittar sammai da kassai (Suna cewa) :"ya ubangijinmu! Baka halicci wannan abu a banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Ya Ubangijinmu! Hakika kai, duk Wanda ka shigar da shi wuta, babu shakka ka kunyata shi. Azzalumai kuwa basu da mataimaka.Ya Ubangijinmu! Hakika mu,  mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa:kuyi imani da ubangijinku. Sai muka yi imani. To ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, ka kuma kankare mana miyagun ayyukanmu! Ka kuma karbi rayukanmu tare da mutane nagari ya ubbangijjinmu! Ka bamu abinda ka yi mana alkawari da shi akan harshen manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alkiyama, Hakika, kai baka saba alkawari. Sai Ubangijinsu ya amsa musu (cewa) :hakika, ni bazan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikin ku, namiji ko mace sashinku daga sashi yake. To wadanda suka yi hijira, aka kuma fitar dasu daga gidajensu, aka cuce su saboda ni, suka kuma yi yaki, kuma aka kashe su, lalli zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar dasu aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinta;(wannan) sakamako ne daga Allah. Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai kiman wadanda suka kafirta a cikin garuruwan ta rude ka. Jin dadi ne Dan kankani, sannan sakamakonsu wutar jahannama ce, tir da Wannan makwanta. Amma wadanda suka ji tsoron Ubangijinsu, Suna da aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu, masu dawwama a cikinsu, wannan liyafa ce daga Allah, abin da kuwa ya zo daga wajen Allah Shi ya fi ga managarta, kuma hakika akwai daga ma'abuta littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abinda aka saukar zuwa gare su, suna masu kankan da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da dan tamanni kankani. Wadancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Hakika Allah mai hanzarta hisabi ne. Ya ku wadanda kuka yi imani! Ku ye hakuri, kuma ku rinjaye kafirce a cikin hakuri, kuma ku ye zaman dako, kuma kuji tsoron Allah ko ku rabauta) (Ali imran, 190 zuwa karshen Surat).


ADDU'AR SANYA SABABBIN TUFAFI 

"Allahumma lakal hamdu anta kasautaniihi, as'aluka min khairahuu wa khaira ma suni'a lahu, wa'auzu bika min sharrihi wa sharri maa suni'a lahu". 

(Ya Allah! Dukkan yabo ya tabbata gare ka, kaine ka tufatar da ni shi (Wannan tufafi) ina rokonka alherinsa da alherin abin da aka yi shi dominsa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinsa da sharrin abin da aka yi shi dominsa.


ADDU'AR SANYA TUFAFI

"Alhamdu lil laahil lazii kasaani haazas (sauba) wa razakaniihi min gairi haulin minnii walaa kuwwatin". 

(Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya tufatar da ni wannan (TUFAFI), kuma ya arzurta ni da shi,  ba tare da wata dabara daga gare ni ba ko wani karfi).


FALALAR ZIKIRI

"Fazkuruunii azkurkum washkuruu lil walaa takfuruuuni. "

(Ku ambace ni zan ambace ku,  ku gode mini kada ku butlce min) (Bakara, aya ta 152)

"Yaa ayyuhal-laziina amanuzkurul-laaha zikran kasiiran wasabbihuuhu bukratan wa'asiila"

(Ya ku wadanda suka ye imani ku ambaci Allah ambato mai yawa kuma ku yi tasbihi don tsarkake shi a safiya da yamma)(Ahzab, ayata 41)

"Wazzaakiriinallaaha kasiiran wazzaakiraati a'addallaahu lahum magfiratan wa ajran azimaa"

(Da masu ambaton Allah da yawa maza,  da masu ambaton sa mata,  Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma(Ahzab, ayata 35).

"Wazkur rabbaka fii nafsika tadharru'an wa khifatan wa duunal jahri minal kauli bil guduwwi wal'aasaali walaa takun minal Gafiliina ". 

(Kuma ka ambaci ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kaskantar da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa),  da safe da maraice, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu) (A'araf, ayata 205).

ADDU'AR DA AKE MA WANDA YA SANYA SABUWAR TUFA

"Tublii wa yukhliful laahu ta'aalaa"

(Allah ya sa ka mayar da ita tsumma, kuma Allah madaukaki ya mayar maka da wata) (Tufar) .

"Iibis jadiidan wa ish hamiidan wa mut shahiidan. 

(Allah yasa) ka sanya sabo, kuma ka rayu kana abin yabo, kuma ka mutu kana shahidi, (wanda aka kashe a tafarkin Allah).

ADDU'AR SHIGA BANDAKI 

"Bismillahi "(Allahumma innii a'uzu bika minal khubus wal kaba'isi"

(Da sunan Allah) ya Allah ina neman tsarinka daga shaidanu maza da shaidanu mata.

ABIN FADI YAYIN CIRE TUFAFI

"Bismillahi ". 

Da sunan Allah.

ADDU'AR FITA DAGA BANDAKI 

"Gufraanaka". 

(Ya Allah gafararka nake nema)

 ZIKIRI GABANIN ALWALA

 "Bismillahi ". 

(Da sunan Allah)

 ZIKIRI BAYAN GAMA ALWALA 

"Ash'hadu an laa ilaaha illallaahu wahdahuu laa sharika lahuu wa ash'hadu anna muhammadan abduhuu wa rasuluhuu". 

(Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, babu abokin tarayya a gare shi;kuma ina shaidawa cewa muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne). 

"Allahummaj'alnii minat-tawwaabiina waj'alnii minal mutadahiriina". 

(Ya Allah ka sanya ni cikin a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin tsarkaka). 

"Subhaanakal -laahumma wabi hamdika ash'hadu anlaa ilaaha ilaa anta wa astagfiruka wa atubu ilaika. 

(Tsarki ya tabbata gare ka ya Allah tare da yabo gare ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, ina neman gafararka kuma ina tuba gareka).


KARANTA:

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 
https://www.facebook.com/netage001/

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor