Idan aka Cire tallafin man fetur zai a jefa talakan Najeriya cikin mawuyacin hali - Sanata Shehu Sani



Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana fargaba da tababa kan makomarsu muddin cire tallafin man fetur baki ɗaya ya kankama nan da wasu 'yan watanni.


Tun bayan samun sanarwar daga gwamnatin ƙasar da ke tabbatar da cewa a watannin farkon shekara mai kamawa ta 2022 za a cire tallafin mai baki ɗaya ake ta tafka muhawara da ce-ce-ku-ce.


Gwamnati dai a ta bakin, Ministar KuÉ—i, Zainab Ahmed ta ce gwamnati ba ta sanya tallafin man fetur da lantarki cikin tsare-tsaren kuÉ—inta na 2022.



Sannan ta shaida cewa a maimakon tallafin mai za a koma bai wa 'yan Najeriya masu karamin karfi tallafin sufuri na naira dubu biyar-biyar a kowanne wata.

Sai dai cikin masu tsokaci kan wannan mataki na gwmanati, kamar tsohon Sanata Shehu Sani ya ce wannan yunkuri zai sake tabarbare lamura da ta'azzara tsadar rayuwa a Najeriya.

Galibin 'yan ƙasar dai ba su karɓi wannan labarin da dadi ba, inda suke ganin cewa matakin zai sake jefa su cikin ƙangin tsadar rayuwa da hauhawar farashi da karuwar talauci.


Mutane da dama na ganin tun da komai kusan kacokan ya dogara kan man fetur, babu mamaki a samu sauyi a farashin kayayyaki, inda dama ke tashin gwauron zabi a kullum a ƙasar.

Akwai kuma masu ganin cewa maye gurbin tallafi da naira dubu biyar ba zai rage raÉ—aÉ—in tsadar rayuwar da ke tunkaro 'yan kasar ba, musamman talaka mai karamin karfi.


Sai dai a tattaunawarsa da BBC, Sanata Shehu Sani ya ce shi bukatar talaka ita ce, kar a kara kuÉ—in man fetur ko da kuwa an cire tallafin ko akasin hakan.


Sanata ya ce cire tallafin na tabbatar komai zai karu, kama daga kudin makaranta da gidajen haya da abinci da kudaden wuta da mkamantansu.


Ya ce akwai hanyoyin da za a iya bi wajen cire tallafin ba tare da talaka ya shiga tasku ba, musamman idan za a raya matatun man kasar da rage kudaden shigo da mai daga ketare.

Tallafin naira dubu biyar-biyar kachal


Sanata Shehu Sani ya nuna rashin gamsuwarsa da tsarin raba wa talaka nair dubu biyar kowanne wata da sunan rage radadin cire tallafin mai.


Sanata ya kare hujjarsa da cewa a Najeriya yanzu naira dubu biyar ba za ta saya wa mutum abin kirki ba ko biyan haya ko sayen abinci.


Ya ce tsarin gwamnati na kare manufarta da sunan samun kudaden yi wa talaka aiki, amma a zahiri karshenta kudaden a karkatar da su maimakon ayyukan cigaban kasa.

Sannan sanatan ya tabo batun kudaden bashi da ake karba a kullum yana mai cewa har yanzu babu wani sauyi in ban da karin matsalolin kan 'yan kasa.


"Galibi karshenta kudin tallafin da aka cire a karkatar da kudade musamman a Najeriyar wannan zamanin.

"Akwai tarin yaudara kan yadda ake tafiyar da lamuran Najeriya, saboda a kullum ana ranto kudaden bashi amma babu wani sauyi.''

A baya dai gwamnatin ta ce ba ta da niyyar cire tallafin man, amma daga bisani ta ce dole ta dauki matakin saboda fatan da ake da shi na kwalliya za ta biya kudin sabulu ya gagara samuwa.


Shugaban kamfanin mai na ƙasar, NNPC, Mele Kyari ya ce gwamnatin na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur.


A ranar Talata Bankin Duniya ya ce Najeriya na buƙatar kawo ƙarshen tallafin man fetur mai matuƙar tsada a cikin wata uku zuwa shida, don inganta harkokin canjin kuɗi da kuma hanzarta sauye-sauye don bunƙasa haɓɓakar tattalin arziƙi.


Alƙalumman Bankin sun nuna cewa kashi 40 cikin dari na talakawan Najeriya, kashi uku kawai na fetur suke amfani da shi a ƙasar, tare da nuna cewa masu arziki ne suke amfana da tallafin mai da gwamnati ke biya.


Najeriya dai ta ce kafin kammala janye tallafin mai a tsakiyar 2022, za ta yi aiki tare da abokan hulÉ—arta kan matakai da suka kamata na rage tasirin janye tallafin ga talakawa.


Sannan adadin waÉ—anda za su amfana da tallafin naira dubu biyar-biyar ya dogara ne ga yawan abin da ke hannu bayan janye tallafin.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor