AMFANIN SHAN ZOBO AJIKIN DAN ADAM








Yadda Shan Zobo Yake Kara Lafiyar Zuciya:




NATURAL ZOBO WANDA BABU KAYAN BATURE:




Acewar wani bincike na shekarar 2010 da aka wallafa a mujallar nazari kan abinci masu gina jiki, an gano cewa yawaita shan Zobo wanda a kimiyyance ake kira Hibiscus Sabdariffa, yana rage hatsarin kamuwa da cutar hawan jini.




Zobo ya kunshi wasu sunadarai da ke taimaka wa wajen sanya nutsuwa a jijiyoyin da ke kai-komo da jini a jikin mutanen da ke daf da kamuwa ko fama da cutar hawan jini marar karfi.

KARANTA:



—Dingyadi Zobo yana rage yawan daskararren maiko wato Cholesterol a jikin masu ta’ammali da shi da wadanda suka mayar da shi abin shan su domin kuwa shi Cholesterol ya kan yi wa zuciya lullubin da zai hana ta aikin da ya dace.




Wani bincike da aka wallafa a ‘Fitoterapia’, wata mujallar tsirrai na magunguna da kuma sanin asalinsu, ya tabbatar da ingataccen tasirin Zobo wajen magance cutar hawan jini.

Kuyi sharing please

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor