Shatu garko ta lashe gasar sanauriyar kyau ta nigeria (miss nigeria]



Shatu Garko, mai shekara 18, ta doke zaratan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma'a da dare a Landmark Centre da ke birnin Legas.


Shatu ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turance.


Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku.


Ta karɓe kambin ne daga hannun Etsanyi Tukura 'yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a 2019.


A cewar masu shirya gasar, wadda ta yi nasara za ta samu kyautar kuÉ—i naira miliyan 10, da zama a gidan alfarma na shekara É—aya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.

KARANTA:

A shafinta na Instagram, matashiyar ta yi godiya ga waÉ—anda suka shirya gasar da kuma waÉ—anda suka É—auki nauyin wannan gasar.


Ta kuma gode wa jama'a bisa goyon baya da kuma soyayya da aka nuna mata



ASALIN HOTON,INSTAGRAM/SHATU GARKO
Bayanan hoto,

Shatu Garko ce Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 44


Masu kula da gasar sun ce ana samun sabbin al'amura a kowace shekara game da matan da ke fafatawa tsawon shekara 44 da ake gudanar da ita.

Wace ce Shatu Garko?


Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 44, Shatu Garko 'yar asalin Jihar Kano ce kuma ita ce ta wakilci yankin arewa maso yammacin ƙasar.


Taƙaitaccen tarihinta da aka bayar a wurin gasar ya nuna cewa tana da shekara 18 da haihuwa, kuma mai tallan hijabi ce da ke ƙaunar hawa doki.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor