Abubuwa Da Ya Kamata Duk Namiji Ya Sani Game Da Mace

 

Wasu Abubuwa Da Ya Kamata Duk Namiji Ya Sani Game Da Mace:


Mata wasu halitta ne da suka bambamta ta ko ina a hali da dabi'u da maza. Amma abun mamaki wasu mazan basu fahimci hakan ba.


Wasu mazan suna tunanin ganin mace tayi mu'amala dasu ne a irin fahimtarsu.


 Wanda hakan yasa maza suke yawan samun matsala da zaran sun soma mu'amala da mace.

KARANTA:

Ga wasu halaye da dabi'un da mata suke da su da ya kamata kowani namiji ya fahimcesu.


1: Mata Sunada Gaggawa: Mata halitatta ne da suke da gaggawa a rayuwarsu. Idan suna bukatar abu basuda jimirin hakurin jiran lokacin abun. Hakan yasa suke aikata wani abun daga baya kuma su dawo suna nadama.


2: Da Son Ransu Suke Auna Abu: Mata basa amfani da hankali wajen auna lamari.

Ita mace muddin abu ya kwanta mata arai to duk abunda za a fadamata akan wannan abun bazata saurara ba.


3: Kalamansu Idan Sun Fusata: Maza da dama sun kasa fahimtar kalaman da suke fitowa daga bakin mace a lokacinda ranta ya baci basu da tasiri a zuciyarta bayan ta huce.


Mace tana iya furta ko wani irin kalma ga mutum a lokacin da ranta ya baci ba tare da la'akari da illar kalmar ba. Amma tana wucewa kuma ko a jikinta. Kai data furtawa kalmar kana kunci ita kuma har ta manta abunta.


4: Bata Saurin Baiwa Namiji Yadda: Mace tana daukan lokaci kamin ta amince da namijin daya nuna yana sonta. Sai dai kuma da zaran ta amince masa babu mai iya bakanta shi a wajenta ta yarda.


5; Batason Wanda Take So Yayi Nisa Da Ita: Mace idan tana son namiji batason yayi nisa da ita. Idan kuma yayi nisa da ita bata samun natsuwar cewa a inda yake bada mace yake ba.


6: Basa Mantuwa: Yana da matukar wahalar gaske mace ta manta abunda kayi mata na alheri ko sharri. Don haka duk namiji ya kula da abunda zai yiwa mace ko zai furta mata.


7: Idan Tana Sonka Matsala: Wani halin da mata suke da shi shine akan soyayya. Idan mace tana sonka masifa ne. Haka idan mace na kinka bala'i ce.


Saboda tsabar son da mace take maka zata iya kasheka ko ta turaka gidan yari. Haka ma idan tana kinka.


8: Game Da Kyauta: Mace idan kana yawan mata kyauta tana maka ganin wawa musamman idan wani abu bai taba shiga tsakaninku ba. Mata suna matukar son mutumin dake musu kyauta, musamman idan sunada ra'ayin namijin.


9: Kambamata: Duk muninn mace tana so kace mata tanada kyau. Babu wani kalmar dake saurin saka mace farin ciki irin ka cemata tana da kyau kuma bata tsufa. 


10: Jima'i: Mace na sha'awar Jima'i ne kadai da namijin datake so ba kaman maza ba. Namiji zai iya Jima'i da macen da baya so domin ya kwantar da sha'awar sa. Mace sha'awar ta na motsawa ne kadai idan tana tare da wanda take so.


Wadannan wasu halayen da dabi'un mata ne daba duk maza suka sansu ba.

SHARE 🔔

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor