Hanyoyi biyar da ma’aurata za su bi idan ba a so ciki ya shiga:
Malaman asibiti a duniya sun bayyana cewa mata da dama za su dauki ciki a wannan lokaci da gwamnatocin duniya suka saka dokar hana walwala domin hana yaduwar cutar coronavirus.
Malaman sun yi hasashen cewa da ga lokacin da gwamnati za ta dakatar da dokar hana walwala zuwa watan Disemba za a samu jarirai da dama da za a haife su sannan wadanda ke da karan kwana a zubar da su tun kafin a haife su.
Wani Likita da ya kware a harkokin jima’i Damian Avar wanda aka fi sani da ‘Sabi doctor’ da yake hira da PREMIUMTIMES ya ce kamata ya yi ma’auratan da basu bukatan haihuwa da wuri su tanadi ko kuma su yi amfani da dabarun bada tazaran iyali da zai kare su daga daukan ciki na tsawon shekaru da dama.
Likitan ya bada wasu dabarun bada tazaran haihuwa guda 5 da ma’aurata za su iya amfani da su a wannan lokaci na hutun dole.
1. KORORO ROBA
Za a iya samun kororo raba a manya da kananan shagunan siyar da magani dake kusa da kai.
Ba su da tsada sannan amfani da su lokacin jima’i na hana mace daukan ciki tare da samar da kariya daga kamuwa da cututtuka.
2. KWAYOYI
Akwai kwayoyin bada tazarar haihuwa da ma’aurata za su iya amfani da su dabam-dabam wanda duk ake samu a kanana da manyan shagunan siyar da magunguna.
Kwayoyin na da sauki kudi sannan idan aka yi amfani da su yadda ya kamata yana hana daukan ciki.
3. ZARE AZZAKARI KAFIN MANIYYI YA ZUBA A FARJIN MACE
Idan ma’aurata ba su tanadi ko kuma basu yi amfani da dabarun bada tazaran haihuwa ba kuma basu son daukan ciki za su iya amfani da dabaran zare azzakari kafin maniyi ya zuba cikin farjin mace.
Wannan dabaran bashi da inganci domin ma’aurata na yi kuka da shi cewa yana rage jin dadi.
Sannan kuma likita yace yin fitsari na taimakawa wajen fitar da maniyin dake dauke da kwayayen halitta wanda idan namiji ya shiga mace ba tare da ya yi fitsari ba mace za ta iya daukan ciki.
4. WASA DA JUNA HAR A FIDDA MANIYI
Ma’aurata za su iya wasa da juna ba tare da sun sadu ba.
Bincike ya nuna cewa wasa na cikin hanyoyin da suka fi gamsar da mace matuka ba sai an sadu sa ita ba.
5. KADA A SADU A LOKUTTAN DAUKAN CIKI
Bisa ga halitta akwai lokuttan da mata suka fi daukan ciki.
Hakan na faruwa ne bayan mace ta gama jinin haila.
Idan namiji ya fahimci haka zai iya kaurace wa matar sa har sai lokacin ya wuce ko kuma a yi amfani da kororo roba idan ya kama.
SHARE.
Post a Comment