
Auren zumunci ko na dangi ba sabon abu ba ne tsakanin kabilu, inda wasu kabilun suke bayar da matukar muhimmanci a kansa domin inganta dangantakar da ke tsakaninsu.
Sai dai duk da auren zumunci da ake yi tsakanin ƴar wa da ɗan ƙane, da kuma makamantansu yana da fa'idoji ta bangaren zamantakewa da kuma ƙara danƙon zumunci, a kimiyance ta ɓangaren lafiya, likitoci sun ce yana da haɗari sosai.
Dr Ibrahim Musa, masanin lafiyar jini a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano a arewacin Najeriya ya ce auren zumunci yana haifar da ƙarin yiwuwar samun cututtukan da ake gada daga iyaye.
Misali, kamar ciwon sikila wanda iyaye sukan kasance suna da nau'in wannan ciwon tare da su, idan aka ci gaba da auratayya ciwon zai ci gaba da yaÉ—uwa.
Sannan masanin ya ce akwai cututtuka da na gado wanÉ—anda auren zumunci ke haifarwa ba tare iyali sun sani ba.
kwayar halittar dangi
Mujallar Lafiya ta The Lancet a 2013, ta ce ƙwayoyin halittar ma'aurata na iya shafar kowaɗanne ma'aurata, komai asalinsu ko ƙabilarsu.
Misali wadda ta auri É—an uwanta da suke jini É—aya za ta fi fuskantar matsala a Æ´aÆ´an da za ta haifa.
Ko da yake a wani cikakken bayani da Hukumar Lafiya Ingila NHS ta yi game da matsalar ta ce ba a cika samun matsala ba a yawancin Æ´aÆ´an da aka haifa ta hanyar auren zumunci, yawanci ana haihuwarsu ne da lafiya.
Amma ta ce auren zumunci kamar na Yar wa da Dan Kane ko YaYan wa da Kanwa, ya fi haifar da matsala ga YaYan da za su haifa da kashi uku zuwa shida, amma kuma matsalar ba mai yawa ba ce.
Ana samu matsala idan ma'auratan biyu sun gaji kwayoyin haliyyar da ke da matsala daga iyayensu.
Me ya sa ƙwayoyin halitta ke da muhimmanci ga dangi
Yan uwa daga dangi daya suna da adadi mafi yawa tsakaninsu na kwayoyin halittarsu. kwayoyin halittar kuma ginshiƙi ne da ke sarrafa jiki.
kwayoyin halittar ne ke daidaita launin ido da girmansa da girman kafafu da hannaye da sauransu.
Ana gadar abubuwa da dama daga iyaye, kamar yadda za mu iya gadar cututtuka da dama daga gare su, ta hanyar kwayar halittarsu.
Wannan zai iya shafar al'ummar da dama, amma ya fi yawa tsakanin dangin da ke auratayya tsakaninsu.
Haihuwar yaya da nakasa
NHS ta ce ana samun matsaloli na gado cikin kowace al'umma a duniya. Kuma al'ummar da ke yin auren zumunci sun fi yawan yaran da ke da matsaloli na gado.
A cewar NHS yan asalin asalin Pakistan a Birtaniya sun fi yin auren zumunci tsakaninsu, kuma tsakaninsu aka fi samun yaran da ake haihuwa da matsaloli na gado.
Matsalar tana faruwa ne idan akwai wata kwayar halitta ta daban a dangi kuma iyayen duka suna da wannan kwayar halittar. Idan a cikin dangin wasu suka auri junansu akwai yiyuwar ƴaƴan da za su haifa su yi gadon wannan ƙwayar halittar daga iyayen biyu.
Dr Ibrahim ya ce tun da cutar tana cikin dangi kuma aka ci gaba da auratayya, ciwon zai ci gaba da yaÉ—uwa daga yayan da aka haifa,
Sauran cututtukan gado da likita ya bayyana da ake samu ta hanyar auren zumunci sun hada da: Ciwon tabin hankali da tawaya ta halitta.
A cewar likitan, bincike ya nuna ciwon na gado na haifar da yawan yin ɓari. Haka kuma yakan iya kara cutuka da ake gada kamar yawan zubar da jini.
Ko a kwanakin baya an gano wasu ma'aurata a ƙaramar hukumar batsari ta jihar Katsina wadanda suka kasance yayan maza zur, wato uban matar da uban mijin Hassan ne da Hussaini, sai suka haɗa yayansu aure.
To yayan nasu ne suka dinga haifar yaya masu tawayar halitta, wato ba su da gurbin idanuwa, sannan wani hancinsa ya kwalmade da sauransu.
To wannan duk ba komai ya jawo ba sai abin da ake kira Fraser II syndrome wato wasu kwayoyin halitta na gado da suke da tawaya da ake samu daga jikin dukkan iyayen biyu da ke da alaka ta jini, kamar yadda Dr Musa ya shaida wa manema labari.
Kansar ido
Auren zumunci kan iya janyo wata nau'in cuta ta kansar ido, kamar yadda tsohuwar babbar jami'ar shirin taƙaita cutar kansa ta Najeriya, Dr. Ramatu Hassan ta bayyana a wata hira da manema labari.
Cutar na fitowa ne a dai dai inda ya kamata ido ya gani, sai a haifi yaro da ita a hankali a hankali tana ci gaba da girma, yayin da yaro ya kamata ya fara tafiya sai ya rika tuntube kamar yadda likitar ta bayyana.
Likitar ta ce auren zumunci ko na dangi da ake yi tsakanin mutane kan yi sanadin a haifi yaro mai irin wannan lalurar.
Kasashen da ke da yawan auren zumunci kamar arewacin Najeriya na da yawan cutar kamar yadda likitar ta bayyana.
Irin wannan cuta ta kansar ido na samuwa ga jarirai tun suna cikin ciki, saboda gado ake yi yawanci, kuma yana faruwa a inda ake yawan yin auren dangi, don haka akwai yiwuwar idan aka ci gaba da auren dangi to kuwa za a ci gaba da samun cutar, in ji ta.
Masana kiwon lafiya sun bayar da shawarwari cewa samun bayanan likita game da kwayar halitta abu ne mai muhimmanci ga dangi.
NHS ta ce Bayanan za su yi amfani ga duk wanda ke da matsala ta gado a danginsa ko kuma wadanda ke da irin wannan damuwar.
Post a Comment