Gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya Rotimi Akeredolu ya bai wa makiyaya kwana bakwai su bar dazukan jihar.
Gwamna Akeredolu ya bai wa makiyaya wannan wa'adi ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin.
Ya bayyana cewa su ne sanadin galibin sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar tasa.
"A yau mun dauki manyan matakai na warware matsalolin satar mutane a hannu daya, da kuma sauran miyagun laifuka wadanda rahotanni kan tsaro da 'yan jarida da kuma wadanda lamarin ya rutsa da su a jihar Ondo suka yi ciakken bayani a kansu," in ji gwamnan.
A cewarsa: "Galibin wadannan matsaloli ana danganta su da wasu bara-gurbi da ke fakewa da sunan makiyaya . Wadannan masu aikata laifuka sun mayar da dazukanmu a matsayin wuraren da suke boye mutanen da aka sace, inda suke tattaunawa domin karbar kudin fansa sannan su aikata wasu laifukan."
Gwamna Akeredolu ya ce a matsayinsa nan babban mai kula da sha'anin tsaro na jiharsa, ba zai zue ido ba ya bari ana ci gaba da aikata irin wadannan laifuka.
"Don haka daga yau Litinin 18 ga watan Janairu, 2021 na bayar da umarnin ga makiyaya su fice daga dukkan dazukan jihar nan nan da kwana bakwai. Haka kuma an haramta yin kiwo da daddare nan take saboda da daddare aka fi lalata gonaki," in ji shi
A cewarsa, sun dauki matakin ne da zummar tabbatar da tsaron rayuka da na kaddarori a jihar ta Ondo yana mai bayar da umarni ga jami'an tsaro su tabbatar da an aiwatar da dukkan umarnin da ya bayar.
Wannan lamari na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin makiyaya da wasu al'umomi da ke kudancin Najeriya saboda zargin da ake yi wa makiyayan da sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa.
Sai dai makiyayan sun sha musanta wannan zargi suna masu cewa wasu gwamnatocin kudancin Najeirya suna yi musu kora-da-hali.
Ko da a makon jiya sai da kungiyar Fulani makiyaya ta Gan-Allah ta zargi jami'an tsaro na kungiyar sintiri ta Amotekun da kashe makiyaya hudu a farmakin da ta kai musu.
Post a Comment