Amfani da na'urar cirar kudi ta POS a Najeriya ya haifar da saɓanin ra'ayi tsakanin malamai da 'yan kasar musamman kan halacci ko haramcin amfani da na'urar.
Yayin da wasu ke ganin cewa amfani da na'urar daidai yake da aikata riba, saboda wani kaso da ake ɗauka daga kuɗin duk wanda ya yi amfani da ita, wasu kuwa na ganin ba laifi ba ne, saboda shi addinin musulunci ɗan sauƙi ne.
Muhawarar ta samo asali ne sakamakon fatarwar da wani malamin addinin musulunci É—an jihar Adamawa Sheikh Abubakar Mukhtar Yola ya bayar game da naurar ta POS.
Mallam Abubakar ya ce amfani da POS don neman kuɗi haramun ne, domin kuɗin da masu POS ɗin ke karɓa a wajen mutane bayan cirar musu kuɗi ya saɓa da shari'a, kuma riba ne.
Duk da cewa malamin ya ce ba laifi ba ne yin amfani da na'urar a wuraren kasuwuanci kamar manyan shaguna da sauransu, wannan fatawa tasa ta janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a Najeriya.
Dangane da hakan ne BBC ta tattauna da wasu fitattun malaman addinin musulunci domin jin tasu fatawar game da wannnan batu.
Shiekh Aminu Daurawa Fitacen malamin addinin musulunci a Kano ya ce akwai wasu ma'aunai guda biyar a addinin musulunci, wanda duk wani abu da ya taso ake sanya shi a gurbi daya daga cikinsu.
''Akwai abin da yake Wajibi, wato wanda ya zama dole, akwai Haramun, wanda ya haramta, akwai Mustahabbi wanda anso a aikata, akwai wanda yake Makaruhi ne, wato an so a bar shi, akwai kuma Halal, wanda yake ya halatta.''
''A cewarsa maganar POS mu'amala ce ta kuÉ—i tsakanin wani da wani, don haka ita riba tana shiga wuri biyu ne.
Misali mutum ya zo ya ce ba ni canji in baka Naira 100 sai ka ba ni 110, to ka ga an yi canjin kudi iri daya amma wani ya fi wani yawa, to kaga wannan haramun ne'' inji shi.
Ya ce amfani da POS ya halatta, domin dama can mutane na amfani da bankuna, kuma akwai cajin kudi iri iri da ake yi musu, to shi ma mai POS kamar sauƙaƙawa mutane yake, musamman a halin da ba za a iya cirar kudi ko kuma ba za a iya yawo da kudi ba.
Ya kara da cewa kuÉ—in da ake biyan masu na'urar duk lokacin da aka ciri kudi a wajensu ba laifi ba ne, domin yana a matsayin biyansu ladan aikin da suka yi ne.
''Idan da sai ka je wani wajen za ka ciri kudi, sai ya zama a layinku, ko kofar gidanku za ka bada wasu yan kudade a cirar maka ka ga an saukaka maka.
Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ne shugaban majalisar malaman addinin musulunci ta jihar Kano ya shaidawa BBC cewa kai tsaye za ka iya kiran masu POS a matsayin masu yin hidima ga jama'a.
Don haka abin da ake biyansu bayan an ciri kudi lada ne ko hakkin aikin da suka yi, don haka babu laifi a biya wanda ya hidimta maka.
Ya ce matsalar da aka samu ita ce ''Mu a Najeriya mutane ba su gama sabawa da yin hidima irin wannan ba, don haka ake yi wa lamarin gurguwar fahimta.
Ya ce ''Ko kadan babu wani laifi a amfani da POS, hasalima na'urar ta taimaka sosai wajen ragewa jama'a tsananin da suke ciki a baya na mu'amala da kuÉ—i ko cirar kudin a lokacin da suke bukatarsu.
Limamin masallacin Juma'a na unguwar Apo da ke babban birnin Najeriya Abuja, ya ce naurar cirar kuɗi ta POS ta kawo wa al'ummar musulmi maslaha da dama saɓanin baya da sai ka yi doguwar tafiya kafin ka samu bankin da za ka ciri kuɗi, ko kuma biyan buƙatar kasuwanci a duk lokacin da kake buƙata.
Ya ce a wannan lokaci da ake gogayya ta fuskar kasuwanci da kuma nema wa jama'a sauƙi bai kamata wani malamin addunin musulunci ya buƙaci daina amfani da naurar ba, domin kuwa hakan na iya kawo babban naƙasu ga harkokin kasuwancin jama'a.
Sheikh Nuru Khalid ya ƙara da cewa akwai wurare da babu bankuna da yawa, don haka ba laifi ba ne amfani da POS domin taimakawa jama'a a irin waɗannan wuraren
Ya ce a shari'ance, shi kansa mu'amala da banki ya zama larura, don haka kasuwancin da POS wani ɓangare ne na wannan larura, "don haka ba laifi ba ne a shariance wani ya zo da katin cirar kudinsa ka ba shi kudi kuma ka caje shi ladan wahalar da ya yi masa."
''Akwai aminci a cikin harkar, domin banki sun yadda ya caji mai ajiya, shi mai ajiya ya yadda a caje shi, sannan ba wanda ke korafi kowa na jin dadin an taimaka masa, an samu aminci a tsakani ba a cuci kowa ba'' inji Malamin.
Post a Comment