Hukumomin sun bayyana cewa wannan shiri zai dauki 'yan Najeriya 1,000 aiki daga ko wace karamar hukuma 774 a fadin kasar, wanda zai taimaka wajen rage matsalolin rashin kudin da annobar cutar korona ta haifar.
Hukumar samar da ayyukan yi ta kasar ce (NDE) za ta dauki nauyin shirin da kuma aiwatar da shi.
A wata hira da BBC, minista a Ma'aikatar Kwadago ta kasar, Mista Festus Keyamo, ya bayyana cewa domin tabbatar da an aiwatar da shirin cikin nasara, gwamnati ta shigar da shugabannin al'umma da na addinai biyu, da na kungiyoyi masu zaman kansu, da na kungiyoyin direbobi, har da na kungiyoyin mata 'yan kasuwa daga jihohi 36 na ƙasar cikin shirin.
''Wadannan shugabannin addinai su ne za su kafa kwamitoci a yankunansu, wanda zai duba yadda za su tantance wadanda za su ci gajiyar wannan shiri, saboda su suka fi kusa da irin talakawan da wannan shiri ke nufin taimaka wa,'' in ji ministan.
Gwamnatin Najeriyar ta ce, wannan shiri na wadanda ba su yi karatu bane ko kuma ba su da shaidar karatu inda za a dauke su aiki na tsawon watanni uku, kuma za a rika biyan su naira dubu ashirin (N20,000) a ko wane wata.
''Kamar yadda ya kamata ku sani wannna shiri an bullo da shi ne don taimaka wa mutanen da suka dogara da irin abinda su kan samu a kullum, kamar masu ayyukan leburanci da sauran aikin karfi na yau da kullum, da galibi sune annobar cutar korona tafi jefawa cikin mawuyacin hali,'' in ji Mista Keyamo.
Bayan aikin watanni uku menene kuma abin yi?
Mista Kayemo ya ce wannan wa'adi na watanni uku su ake kira 'tsarin yayewa', wand aba wai daga an yaye su shikenan ba, dole a duba yadda za a dora su bisa hanyar da za su cigaba daga inda gwamnati ta tsaya.
''Muna da tsare-tsare da dama a kan teburin mu da muka tanada, wanda muke kira 'tsarin yayewa', saboda bayan watanni uku ka karfafa gwiwar masu karamin karfi a matakin kananan hukumomi - a gaskiyar magana wannan shirin na nufin saka jari a hannuwan irin wadannan mutane ne.
''Akwai wasu mata 'yan kasuwa da jarinsu bai wuce naira dubu 20 zuwa dubu 25 ba, idan ka basu naira dubu 60 cikin watanni uku zai kara bunkasa kasuwancinsu, kun gani an taimaka musu kenan," in ji shi.
Mista Keyamo ya kuma kara jaddada cewa akwai yiwuwar gwamnati ta kara fadada wannan shiri ya zama na shekara-shekara, wanda ya danganta ga irin nasarar da aka samu da kuma yadda aljihun gwamnatin yake bayan watanni ukun.
''Akwai kuma wani shiri da ke kan teburinmu da kokarin ganin an saka wasunsu a fannin ayyukan gona bayan sun kamala watanni ukun, don bunkasa abinci da kuma samar musu da sana'ar yi.''
Ta yaya za ka nemi aiki na shirin ayyuka na musamman 774, 000?
- Ku latsa nan domin ziyartar shafi na ayyuka na musamman da gwamnatin ta tanadar, don samun cikakkun bayanai kan yadda za ku yi rajistar ayyuka na musamman 774,000 ga duka jihohi 36 na jihohin Najeriya da kananan hukumomi 774.
- Sai ku latsa kan jiharku kan taswirar Najeriya da ke kan shafin farko don samun (sunaye da lambobin wayar tuntuba) na mambobin kwamitin.
- Ku zabi karamar hukumarku don ganin matakan da za ku bi daya bayan daya na neman aikin.
Kalli irin ayyukan da za ku iya samu
- Gyara da hakar magudanar ruwa
- Gyara hanyoyin ruwa na noman rani
- Gyaran kananan hanyoyin cikin karkara
- Aikin bayar da hannu a kan titina
- Sharar tituna
- Sharar gine-ginen gwamnati kamar cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu
Post a Comment