Gashi kan fito a wasu sassa daban-daban na jikin dan adam, kuma amfaninsa ya danganta ga bangaren da ya fito a jikin kamar dai yadda binciken masana da dama suka nuna.
Misali, gashi a jikin dan Adam kan fito a sassa kamar Fatar kai, da hammata, da gira, da sama da kasan idanu, da kunne, da hanci, da kasan mara ko al'aura, da gemu, da gashin-baki da kuma kasumba da ke fitowa a gefen fuskar maza wadanda suka kai shekarun balaga.
Baya ga tafin hannu da na kafa, kusan jikin dan Adam a lullube ya ke da gashi, sai dai wasu bangarorin jikin kananan ne da ba za a iya gani sosai ba, amma kuma sun fi yawa a sassa kamar na fatar kai da kan yi tsawo sosai, wanda shi ma ya dangata ga kwayoyin halitta ko kuma jinsi da kabilar da mutum ya fito.
A yanzu ba ma a da ba, gashi na cigaba da taka muhimmiyar rawa a rayuwar dan adam ta fuskoki da dama, idan aka hada da samar wa wanzamai da masu gyaran gashi na zamani karin kudaden shiga saboda muhimmancin da dan adam ke bai wa gashi wajen kawata shi domin kwalliya da kuma nuna ko shi wanene a cikin jama'a.
Ko shakka babu, a ko wane bangare da duniya gashi na da amfani wajen kawatawa da fitar da asali da kwarjini da kuma kyaun dan adam, don haka mutane ba su cika kin kulawa da shi ba.
Hakan ne ya sa wasu kan sarrafa shi ta yadda za a iya gane manufa da kuma sana'a, kamar misali akwai taurarin wasanni kasa da kasa kamar na kwallon kafa, da mawaka, da fina-finai da makamantansu da aka san su da yanayin yadda suke gyara ko kuma aske gashinsu.
Gashi kan sa a banbance jinsin mace ko namiji, matashi ko maashiya, da magidanci, ko kuma dattijo a ko ina a fadin duniya.
Galibi wasu na daukar gashi a matsayin wani abin alfahari da kuma kwalliya ne kawai, kan haka ne za ka ga mutane kan mayar da hankali wajen gyarawa da kuma sarrafa shi ta yadda za su nuna asalinsu da kuma kimarsu.
Abu ne da ake kashe wa makudan kudade don gyara shi, a shafa mai ko a sauya masa launi da sauransu duk dai don nuna isa da asali.
Kana a wannan zamanin mutane kan yi amfani da yanayin gyaran gashin mutum wajen tantance yanayin kabila ko addinin mutum, da halayya da kuma tarbiyya ko mutuntakar mutum.
To amma abu mafi muhimmanci da masana suka bai wa gashi shi ne irin kariyar da ya ke bai wa dan adam ta fuskoki da dama.
1.Gashin jiki
Masana da dama sun yi bincike tare da fitar da bayanai game da muhimmancin da ke tattare da gashi a jikin dan adam, wanda ba kowa ya sani ba.
Sun bayyana cewa gashi na bayar da kariya ga fatar jiki daga barazanar da yanayin muhalli ke haifarwa, tare da karbar sakonni cikin sauri ya kuma sadar da su ta kafofin jijiyoyin kwakwalwar dan adam da zarar ya ji alamar wata barazana.
A wata mujallar kiwon lafiya ta 'Sharecare' ta wallafa bayanan dakta Mehmet Oz, MD na Cibiyar kiwon lafiya ta Presbyterian-Columbia a birnin New York na Amurka da ya nuna cewa jikin dan Adam na da akalla sauwowin gashi 5,000,000.
Hakan ya ce amfanin kowace saiwar gashi shi ne fitar da silin gashi É—aya, kuma gashin kai shi kadai ne na bangaren jikin mutum da ke saurin sauya kamannin dan Adam a zahiri.
Don haka in ji mujallar, yakan bai wa mutum damar isar da sako a yanayin zamantakewarsa.
Dakta Woru Baba Goni, babban daraktan Asibitin Koyarwa na Jami'ar jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ya shaida wa BBC cewa, gashi yana da matukar muhimmanci wajen samar wa da fatar jiki cikakkiyar lafiya da kuma kariya ta musamman daga kwayoyin cuta ko kuma wasu abubuwa da ka iya shiga su yi mata illa.
''Yana da muhimmanci wajen inganta lafiyar fatar jiki saboda ko wane silin gashi a jikin dan adam yana da hanyoyin jini, da jijiyoyi masu aikewa da sakonni zuwa kwakwalwa, da kuma sinadaran da ke tafiyar da kwayoyin halittar dan adam, da kuma kitsen ko man da ke kewaye da shi,'' in ji dakta Goni.
Saiwar gashin in ji masanin, na da nagartattun sinadarin kwayoyin halitta da ke taimaka wa wajen bayar da kariya da samun waraka daga duk wani ciwo ko kujewa a fata cikin sauri, ko kuma wasu abubuwa da ke gurbata muhallinmu kamar kura ko kuma wasu sinadarai da ke yawo a cikin iska.
''Gashi na kare fatar cikin daga illar daga turirin sinadaran da hasken rana ke haifarwa da ake kira, ''ultra-violet rays da kan lalata fata ko ya haifar mata da cutar sankara ko kansa,'' in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, fatar kai na dauke da gashi ne saboda ya kan taimaka mata wajen rike zafi, baya ga akwata dan adama.
''Yana amfani wajen daidaita yanayin zafi ko kuma sanyi a jikin da adam, misali idan a lokacin sanyi ne gashi ya kan kare illolin da sanyi ka iya haifar wa fata jikin dan adam tun kafin ma mutum ya ji sanyin, zai hana isakr ta waje mai sanyi ta rasto kai tsaye ta cikin ita fatar ta aika sako mutum ya ji sanyi sosai.''
Ainihin iskar mai dumi da ke gudana da ke tasowa daga cikin fatar mutum gashin kan hana iskar ficewa daga jiki, ya kan rike zafin yana dumama jiki ya hana jin sanyi sosai, tare da hana iska mai sanyi sosai ratsawa cikin jiki ta yadda za ta iya kawo illa.
A lokacin zafi kuma mutum ya kan rika yawan zufa, saboda zafin wajen zufar kan sayaya jiki saboda gashin kan hana wannan ruwan zufar gudana lokacin zafi.
Gashi a wasu bangarorin jikin dan adam na hana shigar kwayoyin cuta jikin da adam ta yadda za su kawo illa a jikin mutum.
Gashi na aikewa ta sako nan take idan akwai wani bakon abu kamar misali ko sauro ko wani kwaro ko wani abu da zai cutar wa dan adama, mutum zai iya ganewa akwai wani abu bako da ya zauna a kan gasin kafin ya kai ga fatar mutum
Yana hana kansar fata, kamar katanga ko garkuwa ne ya kan hana sinadain hasken rana shiga ciki fatar dan adam ai tsaye da ke haifar da kansar fata.. illa ga fatar dan adam U V Rays.
Masana sun kuma bayyana cewa a da da kuma yanzu, gashi na taka muhimmiyar rawa wajen kare dan adama daga kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.
Ga misali ga nau'in tamatar sauron nan na Anopheles da ke haddasa cutar zazzabin ko irin kwarin nan masu yawo a kasa, ba sa kaunar su ji gashi a jikin dan adama, saboda gashin ya kan yi saurin isar da sako ga jikin dan adam ta yadda asisrin wadannan bakin kwari kan tonu.
Source: BBC
Post a Comment