
Jami'an tsaro a Jihar Kaduna sun yi nasarar ceto mutum biyar da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Birnin Gwari.
Kwamishinan Tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya ce lamarin ya faru ne da tsakar ranar Juma'a bayan dakaru sun samu rahoton cewa wasu 'yan bindiga sun tare hanyar Birnin Gewari zuwa Kaduna.
A cewar kwamishinan, nan take jami'an tsaro suka isa kuma suka yi nasarar tserar da mutanen bayan fafatwa da 'yan fashin.
A wata fafatawar ta daban, jami'an sun kashe ɗan fashi ɗaya tare da kama wani bayan sun buɗe wa motar 'yan sanda wuta.
Aruwan ya ce bincike ya nuna cewa mutanen suna ɗauke ne da makamai domin kai wa 'yan fashin daji a Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja.
Kazalika, rundunar jami'an tsaron haɗin gwiwa ta yi nasarar ƙwato shanu 32 da tumakai 10, waɗanda 'yan bindigar suka sace a Ƙaramar Hukumar Kachia.
DAGA Net Age Blog
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
https://www.facebook.com/netage001/
Post a Comment