Wani dan kasuwa yayi abin da ba'a zata ba a jihar Borno saboda watan Ramadana.
......Ya cire Naira 400 kan kowace katon din taliya wato (spaghetti) saboda alfarman watan Ramadan......
Wani dan kasuwa Mai Suna Bukar Bulama (Bura Dolas) dake nan kasuwar Monday Market ta Birnin Maiduguri yayi abin da ya gagari jiga jigan da attajiran yan kasuwa da Yakamata a ce sunyi a jihar Borno.
Bura Dolas, iya gorgodon karfin sa ya rage farashin taliya wato Spaghetti, da ake sayarwa 4,400 zuwa 4,000 saboda watan Ramadana kuma bazai sayarwa mutum daya sadai kadan kadan saboda kowa ya samu.
A lokacin da wasu mugga daga cikin yan kasuwa suke boye kayan Abinci da sauran abubuwa da akafi bukata a wannan watan da ya kamata aji kan mai karamin karfi su kuma suna anfani da wannan dama dan su kudanci su sami ribar da ba'abu albarka a cikin ta.
ALLAH ya sanya albarka cikin kasuwanci sa ya sakamasa da alkairi Albarkacin Wannan watan mai albarka ga kekkyawan kudurin nasa. Ameen..
Don Allah kuyi sharing, yana barar addu'a awajen bayin Allah.
DAGA Net Age Blog
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
https://www.facebook.com/netage001/
Post a Comment