MAGANIN CIWON HANTA



 MAGANIN CIWON HANTA


Ciwon hanta na daya daga cikin manyan ciwo da yake da wuyar magancewa a duniya amma da Yardan Allah duk Wanda yabi abun da zamu fadi za'a samu waraka da Yardan Allah.


ALAMUN CIWON phantasmagoria


Akwai matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da typhoid akai-akai, haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki mai tsanani, yawan haraswa dakuma tashin zuciya koda ruwa kasha, ido yakanyi yellow, rashin dandano a baki, fitsari ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi ,bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa.


Ga duk Wanda yaji wadannan alamu sai yayi kokarin zuwa asibiti domin Gwaji a daina tsoron gwaji domin magance cutar tana farkonta yafi sauki akan sanda zata tsananta.


Masu ulcer dake yawan ciwon ciki da yawan haraswa da tashin zuciya suna magani basujin sauki suyi kokarin duba lafiyar hantar su domin takan hadu wa masu ulcer sosai.


MAGANIN CIWON HANTA GUDA TARA


1. A samu garin habba cokali 10


2. Garin Sidir cokali 5


3. Garin tin cokali 5


4. Garin bawon kankana cokali 10


5. Garin Citta cokali 1


6. Garin tafarnuwa cokali 1


7. Garin Hidal cokali 5


8. Garin zogale cokali 3


9. Garin Yansun da raihan da kusdul hindi cokali 6


Sai a hadasu waje daya a samu Zuma litter biyu mai kyau sai azuba ciki a juya ya hadu sosai sai a dinga shan cokali uku sau uku a rana.


Fadakakarwa


A guji amfani da nama musamman Jan nama da sauran abun mai ciwon hanta baya bukata.


Don Allah ayi share ko ta ina domin amfanuwar bayin Allah amma kada a chanza mana rubutu domin masu tambaya.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor