Sojojin najeriya sunyi nasaran kama mai yimusu leken asiri


Rundunar Sojojin Najeriya da ke yaki a karkashin Bataliyar Operation Lafiya Dole, sun yi galabar damke wani mai suna Modu Ari a yankin Kamuya cikin Jihar Yobe, wanda ake zargi ya na yi wa Boko Haram leken asiri.

Daraktan Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Yerima ne ya bayyana nasarar damke Ari, cikin wata sanarwa da ya aika wa manema labarai.

Burgediya Janar Mohammed Yarima ya fitar da sanarwar a Abuja, inda ya kara da cewa asirin da Ari da wasu masu hada baki da shi su ka rika aika wa Boko Haram ne ya haddasa asarar da sojojin Najeriya su ka rika fuskanta daga Boko Haram kwanan baya da na kwanan nan.

Yerima ya kara da cewa wadanda ake tuhumar sun amsa laifin da aka tuhume su yayn da aka yi masu tambayoyi.

Ya kara da cewa ana ci gaba da bincike sosai domin ka gano sauran gungun masu yi wa Boko Haram leken asri a duk inda su ke.

“Mummunan ayyukan leken asiri da wdannan mugayen ke yi ya haifar da cikas din kakkabe mabarnata a yankin zirin Timbuktu.

“irin yadda Ari ya rika tona asirin inda sojojin Najeriya su ke ya haddasa Boko Haram samun nasarar kai wa sojoji hari a yankin ba sau daya ba.

” Duk da koma bayan da aka samu, Babban Hafsan Askarawan Najeriya, ya kara jinjina wa dakarun Operation Tura Ta Kai Bango kuma ya yi masu karin kwarin guiwa cewa su ci gaba a jajircewa da nuna kishi wajen bankadowa da kakkabe burbushin ‘yan ta’addar da su ka rage ba a kakkabe ba.”

“Ya hore su kada su yi sako-sako da aikin da ke gaban su, duk kuwa da cewa ana samun wasu batagari masu yi masu yankan baya su na shantale masu kokarin da su ke yi na karasawa da Boko Haram baki daya.”

“Babban Hasfan Askarawan Najerya ya roki ‘yan Najeriya su ci gaba da nuna kishi wajen fallasa duk wani mai alaka da ta’addanci ko mai kai masu rahotonnin sirri.” Inji Yerima.

Source: premium times

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor