Abubuwan dake Janyo yawan hatsarin mota a nigeria



Hadurran mota sun zama tamkar ruwan dare a Najeriya, inda zai yi matukar wahala a yi kwana biyu zuwa uku ba tare da ka ji an yi wani hatsarin mota a kan manyan hanyoyin kasar ba.


Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ce, kusan mutum miliyan 1.3 ke mutuwa kowacce shekara a duniya sakamakon hadurran mota kuma WHO ta ce, matsalar za ta cigaba da karuwa.


Hadurran kan faru ba zato babu tsammani, kuma sukan kasance munana da kan haifar da asarar rayuka. Wani lokaci sukan zo da sauki.

Sai dai duk da haka masana na ganin hadari ba ya faruwa haka nan idan ba tare da wasu dalilai ba da ke haddasa su ba. kuma ko wane hadari da ya danganci sufuri ba zai yiwu a ce ya faru haka nan ba, domin akwai salsala mai karfi.


Raunukan da hadurran mota ke haddasawa su ne aka bayyana ke kan gaba wajen haddasa asarar dimbin rayuka da kuma nakasa a fadin duniya.


Mohammed Kabir Abubakar jami'in wayar da kan jama'a na hukumar kaiyaye haddura ta Najeriya ya bayyana wa BBC abubuwan da ke janyo hadurra ababen hawa a ƙasar inda ya ce an kasa su gida uku kamar haka:

ÆŠabia da halayyar É—an adam (Human factor)
Matsala daga abin hawa (Mechanical factor)
Matsalar yanayi kamar hanya ko ruwa ko zafi ko hazo (Environmental factor)


Jami'in ya ce an fi samun haÉ—urra daga É—abi'a da halayyar É—an adam.


"Yawanci haÉ—arurn da ake samu kusan kashi 90 ya fi faruwa ne daga É—abi'a da halayyar dan adam," in ji shi.


Ya kuma ƙara da cewa, sau da dama a kan fi dora alhakin yawan abkuwar hadurran kan direbobi da hukumomi ke zargin su da kauce wa bin dokokin hanya da na tuki, da kuma rashin mutunta rayuwar bil'adama, wanda ke haifar da hadurran da kan haifar da asarar rayukan jama'a wanda za a iya kauce wa.


Halayyar É—an adam da ke haddasa hadarin ababen hawa a Najeriya su ne kamar haka:

Gudun wuce sa'a ko tukin ganganci musamman a tsakanin matasa
Lodin kayan da ya wuce kima da rashin mutunta dokokin hanya
Tuki lokacin maye ko jin barci ko kuma rashin lafiyar idanu
Rashin girnmama fitilar bayar da hannu wato danja a kan hanya
Bin É“arauniyar hanya
Amfani da wayar salula lokacin tuki
Rashin hakuri
Rashin gogewar tuki gadirebobi


Matsala daga lafiyar abin hawa


Jami'in na hukumar kiyaye haddura ta Najeriya ya ce yanayin lafiyar ababan hawa suna taka rawa wajen abkuwar hadurra.


''Shi ya sa yanzu ya zama aikinmu ne a kullum mu tabbatar da cewa mun duba yanayin motocin da ake hawa kan titina don rage yawan abkuwar hadurra."


Don haka hukumar kiyaye hadurra ke gudanar da aikin tantance lafiyar motoci shekara-shekara a Najeriya," in ji Mohammed Kabir Abubakar.


Ya kuma bayyana manyan matsalolin da suka shafi lafiyar ababen hawa da suka fi janyo hadari da suka hada da amfani da rubabbun tayoyi da rashin kyaun birki.


Matsalar tattalin arziki dai ta sa mutane sun koma sayen gwanjon tayoyi da kayyakin gyaran motocin da su kan su motocin da akasari kan zama babbar matsala da zarar sun fara hawa kan titi.


Matsalolin lafiyar ababan hawa da ke haddasa hadurra sun hada da:

Lalacewar birki
Fashewar taya
Lalacewar injinin mota
Amfani da kayan gyaran mota na jabu
Rashin kyaun fitilun mota ( rashin haske ko kuma masu haske da ya wuce kima)
Rashin gyran mota


Matsalar yanayin muhalli da taswirar hanya


Akwai muhawara da dama game da ko shin a Najeriya lalacewar hanya ita ce kan gaba wajen haddasa abkuwar hadurra a ƙasar.


Wasu na ganin cewa duk da sabbin hanyoyi da kuma gyaran tsofaffin da gwamnatin kasar ke yi hakan bai hana abkuwar hadurra ba, a maimakon hakan ma karuwa ya ke.


Matsalar da ta shafi muhalli na daga cikin dalilan da ke haddassa hadurran ababen hawa kamar haka:

Rashin kyawun hanya
Rashin kyawun yanayi
Kwanoni masu hadari a manyan hanyoyi
Ajiye lalatattun motoci a gefen hanya
Barin dabbobi a sake suna ketara kan titina
Toshe hanya ko kuma shinge


Sai dai kuma duk da muhawarar da ake yi game da batun rashin kyaun hanyoyi a Najeriyar da aka bayyana na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hadurran, da dama na ganin ramukan da ke kan hanyoyin galibi sune suke haifar da lalacewar tayoyin motocin da kan haddasa fashewarsu.



Me hukumomi ke yi


Wata matsala da ta addabi kasashen Afirka a 'yan shekarun nan ita ce ta yawan abkuwar hadurran mota, da ke yin sanadiyyar asarar rayukan dimbin jama'a da kuma nakasa a kusan kowacce rana.


Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya tana kokarin gain cewa an samu raguwa na hadurran ababen hawa musamman a kan manyan hanyoyin kasar,


Hukumar ta ba samar da wani mataki na taimakawa direbobin manyan motcocin dakon mai da na kaya, amfani da wata roba a wajen zuba mai don kaucewa bulbular mai a lokacin da mota ta fadi don gudun kama wa da wuta.


"Duk mako muna fita tashohin mota da masallatai da coci-coci don wayar da kan jama'a game da bin dokokin hanya da kuma kiyaye hadura a kan manyan titinan kasa'', in ji Mohammed Kabir Abubakar jami'in hulda da jama'a na hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya.


Ya ce wayar da kan jama'a game da abubuwan da ke hadasa hadurran mota zai taimaka waje kiyayewa, wanda daga karshe zai iya taimaka wa hukumar wajen cimma burin kula da rayukan masu amfani da ababan hawa.


Ya kuma ce an samu ci gaba game da yawan abkuwa hadurran idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata saboda yanayin yadda suka fadada batun wayar da kan jama'a musamman direbobi.

Source: BBC hausa

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor