bidiyo DA ga shafin jarida na BBC Hausa
Hausawa dai kan ce da gwaji jirgin sama ya tashi; watakila wannan karin magana ta fi dacewa wajen bayyana wata hobbasa da wata kungiya ta yi wajen bude masana’antar gyaran motoci ta mata zallan a birnin Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A mafi yawancin kasashen Africa inda al’adu ke da tasiri kan rayuwar jama’a akwai wasu sana’o’i ko ayyuka da ake ganin sun kebanta ga maza, kamar dai sana’ar gyaran mota.
Matan masu aikin na kanikanci kodayake shekarunsu na haihuwa ba su da yawa kamar yadda adadinsu bai taka kara ya karya ba, sun rungumi sana’ar kanikanci a garejin Nana Female Mechanic Workshop ke son aikewa al’umma babba ne.

Sakon dai shi ne duk wani abu da namiji zai yi mace ma za ta iya yi ,illa dai damar nuna basirar ce ta bambanta.
Matan dai wadanda matasa ne kan fita wurin aiki tun safe har zuwa yammaci inda suke aikin gyaran mota sanye da kayan aikin kanaikanci da aka fi sani da Biri da wando.
Source: BBC hausa
Post a Comment