YADDA AKE HADA DANBUN NAMA



Ayau za mu koyi yadda ake hadin dambun nama cikin sauki.

  • Abubuwan hadawa
  • Nama mara kitse kilo
  • Attarugu
  • Maggi
  • Albasa
  • Gishiri
  • Tafarnuwa
  • Cittah
  • Mangyada
  • Kori

Yadda ake hadawa


Da farko zaki wanke namanki ki sa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa ya nuna sosai.
Idan yayi sai ki sauke ki kawo turminki mai kyau ki daka namanki ya daku sai ki kwashe.


Sai ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki zuba akan dakekken namanki kisa, sannan ki sa maggi da kori ki juya sosai komai ya hadu.


Idan yayi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada ki zuba namanki ki yi ta juyawa har sai yayi yanda kike bukata.
Idan yayi sai ki sauke ki juye a wani abu mai kyau.

Kuyi share da yan uwanku Mata


DAGA Net Age Blog


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH

FUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

https://www.facebook.com/netage001/ 

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor