AMFANIN MAN TAFARNUWA


 AMFANIN MAN TAFARNUWA 

Tafarnuwa tana daga cikin Tsirrai mafiya amfani wadanda duniya ta dade tana amfana dasu.

Annabi (saw) ya tabbatar da cewa tana da amfani sai dai ba ya cinta saboda dalilin warin da take dashi.

Watarana an bashi kyautar wani abinci wanda aka hada da tafarnuwa, sai bai ci ba. Ya aika dashi zuwa wajen Abu Ayyub Al-Ansariy (ra).

Sai Abu Ayyub yace "Ya Rasulallahi kai baka sonshi amma ka aiko min?". Sai Manzon Allah (saw) yace: "NI INA GANAWA DA WANDA KAI BAKA GANAWA DASHI". (Wanda yana ganawa da Mala'ika Jibreelu, su kuma Mala'iku basu son duk wani abu mai wari)

Ga wasu kadan daga fa'idodin da take dauke dasu kamar bincike na masana ya tabbatar

1. CIWON DAJI (CANCER) : Duk mutumin da yake fama da ciwon daji ya yawaita amfani da tafarnuwa. In sha Allahu zai samu waraka.

Idan ciwon Cancer din akan fatar jikinsa ne, sai ya rika shafawa ajikinsa bayan yasha cokali guda tare da zuma.

Idan kuma Sankaran mama ne (Breast Cancer) wanda Mata suke fama dashi, to duk matar da take fama da wannan ciwon ta rika yawan yin girki da tafarnuwa (kamar Jollof rice, ko Pepper Soup, da sauransu). Sannan ta rika shan tafarnuwar wacce aka gauraya tare da Man habbah, kuma tana shafawa ajikin Maman. In sha Allahu zata warke.

2. BASUR : Duk wanda basur yake damunsa, ko yana shan wahala wajen fitar bayan gida, ko kuma masu yin bayan gida da jini, ko masu fama da Kumburin ciki, ko Kaikayin dubura, Ga wani albishir gareku :

Kaje ka samo tafarnuwarka mai kyau. (kamar guda biyu ko uku manya) Ka cire bawon sannan ka bayar a daka maka Fura da ita. 

Ka samu nono mai kyau kasha wannan furar dashi.. In sha Allahu awannan ranar ko washegari duk zaka fitar da basur din dake cikinka. Kuma zaka samu lafiya da izinin Allah.

Sannan ka rika gauraya Man Tafarnuwar tare da zuma kana sha kullum da safe. In sha Allahu kai da basur kunyi sallama.

3. SANYI KO KUMBURIN JIKI : Duk mutumin da sanyi ya kumburashi, ko kuma sanyin ya ratsashi, kullum hancinsa ba ya rabuwa da majina, shima ga albishir :

Ka samo Ganyen Na'a-Na'a ka dafa tare da citta. Sannan ka zuba Man tafarnuwa cokali guda aciki. Ka sanya zuma sannan kasha. 

Haka zaka rikayi har sati guda zuwa kwanaki 10. Kuma kana shafa man tafarnuwar ajikinka In Allah ya yarda jikinka zai sabe, sanyin zai fita, kuma zaka warke.

4. SANYIN QASHI RHEUMATISM) : Masu fama da sanyin Qashi ko kuma Rikewar gabobi (Arthritis) ga naku :

Ku samo Man tafarnuwa mai kyau, ku gaurayashi da Man Habbatus sauda, Sannaan a dorashi bisa wuta mai ci ahanakali. Idan yayi kamar minti biyar sai a sauke. 

Wannan man mai dumi Za'a rika shafawa ajikin Qafar, ko bayan, ko kwankwaso, ko Qafar da take ciwon. In sha Allahu ko da ciwon bayan yafi shekara goma ana fama, to za'a samu lafiya da izinin Allah.

5. HAWAN JINI DA CIWON ZUCIYA : Bincike ya tabbatar da cewa tafarnuwa tana narkar da mummunan kitsen nan na Cholesterol wanda shine yake toshe Kofofin zuciyar Dan Adam, har ake samun hawan jini ko ciwon zuciya. 

To tafarnuwa tana narkar dashi kuma tana bude duk hanyoyin da suka toshe din. Sannan tana tsaftace jinin jikin Dan Adam.

Ana so masu fama da hawan jini suyi wannan hadin domin samun kuzari da lafiya :


A samo ganyen Zogale danye adafashi tare da tafarnuwa. Bayan an taceshi kafin asha sai a sanya Man Zaitun cokali guda, asanya zuma sannan asha. Kuma ayawaita cinta acikin abinci yau da kullum. In sha za'a dace.


6. TYPHOID FEVER (ZAZZABIN HANJI) DA KUMA ULCER : Duk masu fama da wannan larurar ga magani nan da yardar Allah : Ka rika shan cokali guda na tafarnuwa gauraye da zuma kullum da safe, minti 30 kafin breakfast. 


In sha Allahu wannan zai kashe duk kwayoyin chutar dake cikin cikinka. Hakanan masu macijin ciki ko Tsutsar ciki su ma tsotsotsin zasu mutu. Kuma zasu fita da izinin Allah. 


Hakanan masu fama da gyambon ciki (Ulcer) su ma zasu samu saukinta idan suka bi wannan hanyar. Kuma su rika sanya cokali guda dlna man tafarnuwar acikin dukkan abincin da zasu ci. Ko kuma arika dafa abincin tare da ita.


7. CIWON HANTA : Tafarnuwa tana bama hantar 'Dan Adam kariya daga chutattuka. Kuma amfani da ita yana hana kitsen nan na cholesterol taruwa ko ginuwa ajikin hanta, ballantana har a samu matsalar ciwon ciki ko Kumburin Hanta.


Masu ciwon hanta su rika shan man tafarnuwa ko garinta wanda aka chakuda da zuma. In sha Allahu Za'a ga abun mamaki wato samun lafiya cikin Qankanin lokaci. 


Wannan Sadaukarwa ce daga Net Age Blog Duk wanda ya jarraba ya dace, tukwicinmu akansa shine yayi Salati da Tasleemi guda goma ko sama da haka ga Ma'aikin Allah (saw). Kuma atura ga yan uwa da abokai.

DAGA Net Age Blog


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH

FUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

https://www.facebook.com/netage001/ 

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor