YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA DA BIKI



YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA SAURANSU.

Daga: Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam [Rahimahullah].

(Malam ya yi wannan bayanin ne a Tafsirin Maiduguri na shekarar 2006M a cikin Suratut-Taubah aya ta 100)

“Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).

Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan ka zo za ka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da za ka fara yi shi ne:

Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gabanka, a dai-dai lokacin da za ka wanke gabanka a lokacin za ka kulla niyya ta wankan Janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana ka yi tsarki kenan, to daga nan kuma sai ka yi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah za kayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan za ka kyale shi ba za kayi shi ba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko ina a kanka.

To idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikinka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko ina. To idan ka yi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne sai ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka ta hagu shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan Janaba.

In wankan Janaba ne haka za ka yi, in na Haila ne haka za a yi in ma wanka ne na Biki haka za ayishi.

Me karatu Don Allah kayi sharing zuwa group group, wannan sadaqatul jariya ce, ubangiji Allah yakai ladan kabarin iyayenmu Amen.

DAGA Net Age Blog


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH

 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

https://webook.com/netage001/ 

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor