AMFANIN DABINO AJIKIN DAN ADAM


AMFANIN DABINO (Date fruits)

Dabino yana daya daga cikin kayan itacen da Annabi (saww) ke so.

1. Yana saurin narkarda abinci

2. Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure

3. Yana taimakawa wajen kara jini

4. Yana taimakawa Ma'aurata maza/mata

5. Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi. 6. Yana karawa Ido lafiya

7. Yana Rage Nauyin kiba da teba.

8. Yana Maganin Gudawa

9. Yana Saurin Saukarda Hawan jini

10. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun basira..

11. Yana kariya daga Sihiri

12. Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun sauqi wajen haihuwa.

13. Yana kariya daga Sihiri.

YADDA ZA'AYI AMFANI DA DABINO. CIWON NONO GA MACCEN DA TA HAIHU

Ana cin dabino guda 7 asha man tafarnuwa karamin cokali sau 1 arana kwana uku.

DOMIN SAMUN NI'IMA GA MA'AURATA;

Ana daka dabino a zuba cikin madara (freesh milk) sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya kafin a kwanta. GA MATA MASU JUNA BIYU; Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan anyi kusan haihuwa Wannan yana hanawa macce yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin Allah.

GUDAWA;

Ana daka garin dabino a saka a ruwan zafi a sha In shaa Allahu yana tsayar da gudawa.

SAMUN KUZARI;

Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1 da safe da yamma.

SAMUN LAFIYAYYAR FATA;

Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska awa daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan yana saurin gyara fuska. Bin cike ya nuna Yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon CANCER ko wacce iri.

👉Haka Kuma MANZON ALLAH (saww) YACE DABINO AJWA YANA MAGANIN DUKKAN CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA KACISHI,BABU WATA CUTA DA ZATA SAMEKA AWANNAN RANA, KO KUMA SAMMU KO SIHIRI. Wasu MALUMMAN MUSULUNCI kuma sunce Annabi (saww) Yana nufin kowanne dabino ba wai sai Ajwaba (Wallahu A'alam)
Allah Ne Masani

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor