YADDA AKE YIN MAN CARAS DA AMFANINSA




MAN KARAS " CARROT OIL RECIPE"

.

1- Karas Manya "Iya Adadin Man Da Ake San Samu'

2- Man Kwakwa Ko ,Man Zaitun "Ko Kuma Duk Man Da Ake Dashi, Amma Ya Zamto Mai Kyau Ne.

2- Potato Peeler,

3- Grater

4- Kwalba Mai Murfi " Jack Buttle"

.

PROCEDURE "YANDA ZA A HADA"

.

Mataki Na - 1

- Za a wanke Karas sosai, sannan a tsane ruwan da yake jikinsa na wankewar, kana a ajiye a waje guda.

.

Mataki Na - 2

- Za a dauko Potato Peeler sai a kankare bawon da yake jikin bayan Karas din. Za kuma a yi hakan ne a duk iya adadin yawan Karas din da ake san yin amfani dasu, idan an kammala, sai a sake wankewa a ajiye a waje guda.

.

Mataki Na - 3

- Za a dauko Grater ( Ana yin amfani ne da sashin gidagen da yafi kowanne sashi kananun hudoji ) a dunga daukan Karas din daya bayan daya ana kankarewa har a kammala.

.

Mataki Na - 4

- Za a dauko Jack Buttle sai a zuba Karas din da aka kammala Kankarewar a cikinta, sannan kuma sai a dauko Mai (Na Zaitun Ko Na Kwakwa) iya adadin da ake dashi sai a zuba a cikin Kwalbar da aka zuba Karas din, sannan sai a juya da Cokali. Amma a tabbatar sun hadu sosai da juna, duk da hakan a kara jijjiaga Kwalbar sosai




.

Mataki Na - 5

Za a zuba ruwa a cikin Tukunya, ( Ba cika Tukunyar za a yi ba, kadan kawai ) sannan a dora akan Risho, a bar ruwan ya tafasa, sannan sai a rage yawan wutar daga 'kasan Risho din, sai a bude murfin da aka rufe Tukunyar Ruwan, sannan sai a dauko Kwalbar da hadin Karas din yake ciki sai a dora a cikin tafash-shen ruwan ( Murfin Kwalbar dorawa kawai za a yi a samanta, kada a rufe 'kam-'kam gudun kada Kwalbar ta fashe a ciki ) Sai a dauko murfin Tukunyar da aka tafasa ruwan ita ma sai a rufe Tukunyar da shi. Za a barshi na tsahon mintuna 10 kacal kafin a bude, a cire Kwalbar daga ciki.

.

Mataki Na - 6

- Za a ajiye Kwalbar a waje guda har zuwa lokacin da za tayi sanyi, hadin Karas din da ke cikin ta shima zayyi sanyi. To daga nan sai a sake sanya Cokali a cikin Kwalbar a juya sosai da sosai, a kuma sake jijjaga Kwalbar sosai.

.

Mataki Na - 7

- Za a sami rariya mai fitar da laushi ( Irin 'Karamar nan ) sai a taje man da ke cikin Kwalbar a cikin mazubi mai tsafta, domin a fitar da duddugar Karas din ita ma daban.

.

Mataki Na - 8

Wannan shi ne Man Karas din ku ( Carrot Oil ). Sai ku zuba a cikin Kwalba ku rufe ku ajiye kayan ku domin duk amfanin da ku ke san yi dashi.

.

WASU DAGA AMFANIN SA.

.

AMFANIN SA A CIKIN ABIN CI.

1- Inganta Lafiyar Ido

2- Garkuwar Daga Kamuwa Da Canser

3- Gyaran Fatar Jiki

4- Taimakawa Masu Ciwon Sugar

5- 'Karfafa 'Kashi

6- Cutattukan Baki Da Hakori

7- Inganta Lafiyar Hanta

8- Rage Kishe

9- 'Kara 'Karfin Garkuwar Jiki.

0- Yana 'Kara Ruwan Nono Ga Mata.

.

AMFANINSA A GASHIN KAI DA KUMA FATA

1- Yana Taimakawa Gashin Kai Ya Zamo Da Danshi.

2- Yana Taimakawa Fatar Kai Ta Zamto Da Laushi

3- Yana Taimakawa Gashin Kai Yin Tsayi Da Sauri

4- Yana Hana Gashin Kai Karyewa

5- Yana Sa Fata Tayi Haske

6- Yana Sa Fata Tayi Laushi

7- Yana Gusar Da 'Kurajen Da Suke Fitowa Fata.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor