AMFANIN JIMA'I GA MA'AURATA

 



1. RAGE HAWAN-JINI :


Abisa wasu bayanai masu inganci da muka tattaro na wasu masana kimiyya, yin jima'i tsakanin ma'aurata na taimakawa wajen rage hawan-jini a lokacin da yake hauhawa.


2. HUCE WAHALA:


Idan maigida ya dawo aiki ya shawo wahalar aikin ofis, ta kasuwa ko wata wahala mai wuyar gaske kuma ya naso ya huta, toh sai yayi

wanka, yaci abinci, ya kuma sha ruwa ko lemu,sa'annan ya sadu da iyalinsa. Ko shakka babu zai samu wani irin hutu da bacci mai dadi da kuma debe wahala. Jima'i na rage 'stress' da 'pressure' sosai.


3. KARFAFA GARKUWAR JIKI:


Binciken wasu masana kimiyya ya nuna cewa,mutane (magidanta) masu yin jima'i akai-akai sunfi yawan sinadarin "antibody" a cikin jikinsu fiye da wanda basu yin jima'i kamar yawan nasu. Shi dai wannan sinadari amfaninsa shine kare jikin 'dan adam daga cututtuka (germs,viruses and other intruders) masu kai farmaki a cikin jiki su cutar da lafiya- wato garkuwane ga jikin 'dan adam . Toh saidai yana da kyau mutum ya yawaita cin abincin dazai kara masa lafiyar jima'i kamar yanda muka bayyana a can baya . Kuma mutum ya rinka hutawa don samun cikakkiya lafiya da ni'ima.

4. GYARA MANIYYI:


Mutum mai saduwa da iyalinsa akai-akai, ilimi ya nuna cewa maniyyinsa na kara inganci da lafiya. Zaya samu sabon maniyyi ya zubda tsohon maniyyi. Hakan zai iya taimakawa sosai wajen saurin samun juna biyu ga iyalinsa. Haka kuma, sabunta saduwa da uwargida na kara mata sha'awa da ni'imar ruwa (vaginal lubrication) domin saduwa da maigida cikin sauki da santsi. Wannan rahotone daga wata mai ilimi akan kiwon lafiya (Assistant clinical professor of obstetrics and gynecology at Northwestern University's Feinberg School of Medicine in Chicago).


5. RAGE CIWO:


Jima'i na rage radadin ciwo kamar irin na ciwon jiki ko na baya da sauransu. A lokacin da mutum yayi inzali, jikinsa na samarda wani irin sinadari (hormone oxytocin), wannan sinadari yana taimakawa sosai wajen samarda wani sinadarin kuma (endorphins) wanda keda tasiri kamar na maganin "aspirin" da "panadol" (pain relievers) masu rage zafin ciwo. Jima'i magani me mai karfi na ciwo. Idan mutum yanaso ya gane gaskiyar wannan zance, a lokacin da yake jin wani ciwo a jikinsa, ya saurara yaji idan akwai ciwon lokacin yake kawowa (inzali).


6. GYARA ZUCIYA:


Masana kimiyya sun bayyana jima'i a matsayin wani nau'in motsa-jiki (exercise). Motsa jiki nada muhimmanci sosai ga lafiyar mutum. Yana gyara lafiyar zuciyar 'dan adam da kuma kare ta daga cututtuka masu kai farmaki. Yana sanya gudanar jini a zuciya da sauran jiki yanda ya kamata domin samun cikakkiyar lafiya.


7. RAGE KIBA:


Yawan jima'i nasa rama. Kada mu manta da cewa jima'i wani nau'i ne na motsa-jiki.Yana kone sinadaran kuzari (calories) wanda taruwarsu da yawa a jiki ba tare da amfani dasu ba ke jaza kiba (weight gain). Jima'i na tsawon rabin awa na kone/amfani da kimanin 75 ko 150 na

sinadarin. Anyi kiyasin cewa mutum na kone sinadarin kimanin 129 yayinda yake tafiya a kasa tsawon rabin awa.Yawan kiba nada illa sosai ga lafiya. Yana haddasa ciwuka kamar na zuciya, ciwon

suga da ciwon kafafu ko gabbai. Toh masu kiba ga wata dama ta samu - Jima'i hanyace ta rage kiba.


8. GYARA FATA:


Fata tayi kyau da kala mai kyau mai alamun lafiya.


9. GYARA MAFITSARA:


Yana gyara lafiyar mafitsarar mata domin rike fitsari da sauransu dai mutakaita.


Wadannan bayanai da suka gabata basa yin nuni cewa mutum ya yawaita yin jima'i da iyalansa. Yawan yin jima'i na iya sanya mutum

ya tsotse ya kuma rasa wasu sinadarai masu muhimmanci a jikinsa. Nemi Karin bayani daga malaman addini da kuma likitoci akan a dadin

yawan jima'i da mutum yakamata ya rinka yi a sati don cikakkiyar lafiya da ni'ima. To amma adadin yawan a sati yasha bamban tsakanin mutane ta fuskar shekarunsu, yanayin halittar su da kuma lafiyarsu da kuma wasu sauran dalilan na daban.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH

FUKANMU NA SADA ZUMUNTA 
https://www.facebook.com/netage001/

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor