Magungunan Gyaran Jiki guda goma sha shida (16)


 Magungunan Gyaran Jiki.


Auratayya tafi armashi idan ana duba lafiyar jiki da gyara jikin


1. Maganin gyaran fata

Ki samu;

Ruwan cikin kabewa (quater cup),

Madara (quater cup),

Zuma babban cokali (1),

Qwai qwaya daya (1),

Ki hada ki cakuda ki shafe cikin ki na tsawon minti ashirin 20mins ki wanke da ruwan zafi. Zaki sha mamaki.


2. Maganin rage qiba

A samu;

Zuma,

Garin habba,

Tafarnuwa qwaya daya,

A hada garin habba babban cokali daya da tafarnuwa a daka su a zuba zuma a cikin rabin kofin ruwa ana saha kafin a ci abinci da safe da kuma idan za'a kwanta da misalin minti ashirin 20mins tsawon kwana arba'in da biyar (45days). Yana maganin hawan jini, rashin yin fitsari ko jin zafi idan ana fitsari, ko kasala da ciwon ciki mai tsanani.


3. Maganin qarin jiki, girman hips, ruwan nono, tsayuwar nono da laushin jiki gabadaya.

Ki samu;

Dankalin turawa (irish),

Madarar shanu (pure),

Zuma.

Ki dafa dankalin yayi laushi sosai, sai ki dama shi da madarar shanun kamar yadda ake dama fura da nono, sai ki zuba zuma kadan. Zaki dama iya adadin abin da zaki iya shanko dankali nawa ne. Kiyi haka sau daya kullum har rsawon kwana arba'in (40 days).


4. Magani ciwon sanyin mata / maza (infection).

Namijin goro (5),

Citta mai yatsu (5),

Tafarnuwa (4),

Zuma mai kyau,

Lemon tsami (5),

Sai a yanka lemon tsamin a tafasa da bawon sa tare da sauran kayayyakin, sai ana sha kaman shayi rabin kofi sau uku a rana na sati 2.


Ko kuma

Namijin goro,

Tafarnuwa,

Citta, 

kanimfari,

Kajiji,

Masoro,

Zuma,

Hada wadannan ku tafasa sai ku zuba zuma idan zaku sha kamar shayi sau 2 na kwana 3 ko sati daya.


Ko kuma, ga sanyin mata, a samu;

Bagaruwa,

Lalle (garin ko ganyen),

Ganyen magarya,

Habba,

Kanimfari,

Hulba,

Ki hada wadannan ki tafasa, sai kina zama a cikin ruwan da dumi daidai yadda zaki iya tsawon minti talatin 30mins, kiyi kaman sati daya. Wannan maganin infection ne da matsi.


Ko kuma

Ki samu qaron ararrabi ki jiqa shi ya tsimu da ruwa sai ki zuba ma'ukhal ki jijjiga. Amma idan kina da ulcer ki sa ma'aukhal din kadan. Zaki sha cokali daya sau 2 a rana na kwana 3 ko sati daya. Indai sanyi / infection ne kunyi bye_bye in shaa Allah.


Ko kuma

Ga matsalar infection, zaki iya tafasa ganye ko garin lalle, sannan a ringa tsarki da shi ko a zauna a ciki lokaci zuwa lokaci, za'a iya yiwa yarinya yar shekara daya idan matsalar infection ce.


TSOKACI: Idan za'a sha maganin sanyi / infection yana da kyau ku sha ke da maigidan ki in ba haka ba daya zai iya dauka ya gogawa daya.


5. Maganin basur.

Ku samu;

Garin habba,

Garin Ruman,

Garin tafarnuwa,

Zuma.

Ku hada wadannan ku cakuda da zuma ku sha cokali daya, sau biyu a rana. Tsawon sati biyu.


Ko kuma, ku samu;

Man habba,

Man tafarnuwa,

Man albasa,

Man zaitun,

Man hulba,

Man na'a na'a,

Ku hada su ko ku sha daban daban kaman yadda ake shan maganin asbiti qaramun cokali sau uku a rana.


Ko kuma a samu;

Garin habba,

Garin ruman,

Garin hubba,

Garin zogale,

Zuma,

Za'a hada wadannan ana sha cokali daya sau uku a rana.

Tsokaci: a yawaita shan ruwa da cin ganyayyaki zai taimaka sosai.


6. Gyaran Nono idan ya saki ko ya lalace.

Ana buqatar wadannan abubuwa kamar haka;

Danyar shinkafa, 

Alkama, 

Ridi, 

Hulba, 

Busashshiyar ayaba, da kuma

Aya.

Za'a hada wadannan kaya a malkada baki daya suyi laushi kamar gari, banda Aya. Ita ma za'a malkada ta daban a a tace ruwan ta sai a hada a dama wancan garin da ita kamar yadda ake dama kunu lokaci zuwa lokaci daidai buqatar ki.

Wannan qwarai da gaske zai taimaka wajen cikowar nono da lafiyar sa. Amma ga matan da suka taba haihuwa / shayarwa kenan.


Ko kuma, ki samu;

Nonon jar akuya (cokali 5),

Zuma (cokali 2), 

Jar kanwa yar kadan,

Sai ki shafa idan zaki kwanta a nonon ki, sannan idan kin tashi da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafe shi da man hulba. Wannan na gyara nono ko na budurwa ko bazawara ko me shayarwa. Kici gaba zuwa wani lokaci.


Ga budurwa ko macen da bata taba haihuwa ba.

Macen da take son gyara tsayuwar nonon ta, za ki samu HULBA mai kyau kina sha sau hudu a rana. In shaa Allahu za ki sha mamaki.


7. Maganin bushewa ko qarancin ni'ima / sha'awa.

Ga macen da take bata da sha'awa ko qarancin ni'ima ko bushewar gaba.

Ki samu lemon zaqi guda 5 ki matse ruwan a kofi, sai ki danqi kannfari dan kadan misalai kaman da yan yatsu 3 ki jiqa kaninfarin har tswon minti 30 a ruwa cikin qaramin ludayi ko quater kofi, sannan ki taceshi ki zuba cikin ruwan lemon ki juya, sai ki sa zuma dan kadan rabin karamin cokali ko sugar dan kadan ki sha tsawon sati daya. 


Ko kuma

ki samu wadannan abubuwa kamar haka;

Man habba,

Man hulba,

Man na'a na'a,

Man tafarnuwa da kuma

Zait Lauz.

Za'a hada wadannan abubuwa daidai gwargwadon adadi, sannan a shanye take. Amma da zarar kin sha DOLE ki tashi ki tsaya a tsaye na tsawon minti sha biyar (15minutes).


TSOKACI!

Game da TAFARNUWA - tana da tasirin gaske wajen abin da ya shafi matsalar sanyin jijiya da mara, KUSKURE ne cin ta, ko hadiyar ta domin hakan na iya bayuwa ta shanye ruwan cikin mutum har yakai shi ga halaka. Maimakon haka zaifi kyau cin ta dafaffiya, ko da nama ko a abinci ko man ta, ba cinta zallah ba.


Wajen amfani da wannan magani dole mace ta tsaya a tsaye na tsawon 15mins kuma kada taci komai a wannan lokaci domin bawa wannan magani dama yayi aikin sa yadda ya dace, kuma mace na iya fuskantar juyawar ciki ko mara da zubar da wani ruwa daga gaban ta tare da jin sha'awa musamman idan tana da larura a mara / cikin ta.

Kada mace mai al'ada ko wacce al'ada ta kusa zuwa mata yau ko gobe ta sha wannan maganin domin hakan na iya jawo mata matsala.


Ko kuma

Ki samu nonon raqumi cikwi ki hada da madarar shanu ki juya ki sha banda suger, sa'annan ki ci ayaba ko da guda uku ce har tsawon kwana 3 ko sati 1.


8. Maganin matsi ingantacce na mata.

Zaki samu man tafarnuwa da man zaitun da zuma ko wanne rabin cokali ko cokali, sai ki sa auduga ki dangwala kisa a gaban ki har tsawon minti 15mins sau daya kullum.


Ko kuma

Ki samu garin bagaruwa ki tafasa, sai ki zuba alif kadan, sannan ki zuba farin miski a ciki idan ya huce sai ki ringa tsarki da shi har tsawon wani lokaci.


9. Maganin gyaran Azzakari da qarin ni'ma.

Yawaita cin ganye a abincin ka koda yaushe, musamman ganyen LANSIR zaka sha mana yadda lafiyar zakarin ka zata kasan ce.


Ko kuma

Samu ayaba da madara (peak ko luna) a dama su da zuma ana sha zai taimakawa samun ni'imar ki/ni'mar ka.


Ko kuma

kaci ayaba biyu zuwa uku kafin ka sadu da iyalin ka da minti talatin (30mins), amma kar sai ka cika cikin ka da abinci, ta zamo kafin cin abincin da minti 20mins tsawon wani lokaci.


Ko kuma

Ka sha kankana yadda zata isheka, amma ka cinye da farin jikin bawon da kuma qwallon ta kafin kaci abinci da minti ashirin 20mins, kafin ka sadu da matarka da minti talatin 30mins. Tsawon wani lokaci.


Ko kuma

Ka ci namijin goro a qalla guda biyu kullum tsawon wani lokaci. Za'a samu qarfin azzakari da yardar Allah.


10. Qanqancewar Azzakari

Samu man zogale kana dangwala dan kadan da auduga kana shafe Azzakari ka safe da yamma amma banda kofar fitsarin ka tsawon wata guda, saidai kada ka shafa da yamma idan kasan zaka sadu da matar ka.


Ko kuma

Samu man kwakwa da kanumfari ka cakuda su kana shafawa a azzakarin ka safe da yamma amma banda kofar fitsarin ka tsawon wata daya.


Ko kuma

Samu nonon raqumi ²/3 na kofi ka zuba garin habba cokali daya da zuma cokali daya kana sha sau biyu a rana tsawon wata guda.


11. Maganin warin baki

Mai da zuma a matsayin MacLean din ku, kuna brush dashi in sha Allah za'a dace.


Ko kuma

Jiqa kanimfari kuma brush da ruwan sa, zai taimaka qwarai wajen warin bakin har ma da matsalar ciwon haqori.


12. Maganin warin gaba (Farji)

Ki ringa tsarki da zuma har misalin tsawon kwana 3 ko sati 1 sannan ki guji zama babu fant, in sha Allahu za'a dace.


13. Maganin amosani

Samu garin ganyen magarya cokali 2 ku tafasa a cikin kofi 5 na ruwan zafi, da zarar ya huce ku ringa wanke kan ku, ku tabbata ya gama ko ina. Bayan ya bushe sai ku shafa man zaitun mai kyau. Ku aikata wannan har tsawon sati daya ko biyu (1-2 weeks) in sha Allahu za'a dace. 


Ko kuma

Ku samu zama mai kyau ku shafa iyan yakai tsawon minti 15-30mins sai ku wanke da ruwan dumi sannan ku shafe shi da Zaitun, shima zai taimaka.


Ko kuma

Ku samu albasa ku malkada sannan ku tace ruwan ta sai ku hada da zumar ku mai kyau ku cakuda sannan ku shafa a kan ku, bayan minti 15mins ku wanke da ruwan dumi (za ku iya sa sinadarin wanke kai), idan ya bushe sai ku shafa Zaitun, tsawon sati 2 (2weeks). Za ku sha mamaki in sha Allahu yadda gashin ku zaiyi baqi, tsawo, da qwari sannan yana futo da gashi ga masu sanqo ko qara yawan gashi ga masu buqatar qari.


14. Maganin fitsarin kwance

Garin habba,

Garin hulba,

Qustatul hindi,

Tsamiya,

Zuma,

Za'a tafasa wadannan a zuba zuma, sai a bawa mai fitsarin kwance da safe kafin ya karya da kuma idan zai kwanta da daddare. Wannan yafi ga manya.


Ko kuma

Garin habba,

Nono ko madarar shanu,

Za'a hada a gwauraya sai ana sha, amma idan madara ce sai an dumama ta.


Ko kuma

A samu zuma mai kyau a ringa bawa yaron cokali daya babba kullum ko qaramin cokali sau uku a rana. Wannan yafi musamman ga qananan yara.


15. Maganin HIV

Garin citta (cokali 10),

Garin zogale (cokali 10),

Garin Ruman (cokali 10),

Garin habba (cokali 25),

Zuma (lita uku),

A hada a cakuda ana sha uku sau uku na wata 2 ko kwana sittin daidai. Sai aje ayi test.


16. Maganin cin ruwa

Samu lalle ki kwaba ki sa a wajen dake cin ruwan har tsawon minti talatin 30mins sai ki wanke, zaki rabu dashi in shaa Allah.

FUKANMU NA SADA ZUMUNTA 
https://www.facebook.com/netage001/

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor