Yadda ake kasuwanci cryptocurrency



WHAT IS CRYPTOCURRENCY 

Mutane da dama musamman Bakin wannan harka wato (Newbies) zakaga sunata mamaki Idan sukaga wani Ya kawo musu tallan coin Kuma yace suyi bincikensu kafin su siya sabida su basusan ya akeyi ba wajen Gane ingancin nasa, toh ka duba Insha Allah zaka qaru.


Kafin mushiga ciki, sabon Dan Crypto akwai wata yar nasiha dazanyi maka:


Abu Na farko, kasaka a ranki Crypto market ba gurine da ake samun kudi cikin sauki ba.


Abu Na biyu, ka tabbata ka koyi yadda ake siya Koh siyarwa da kanka a Dukkan kasuwannin Crypto both CEX & DEX.


Abu Na uku, Ka kiyaye siyan coin Koh token a wajen Wanda baka sani ba, koda kuwa wanne irin coin ne. a takaice dai ya zame maka Dole ka koyi yadda ake siya Koh siyarwa da kanka, idan ba Haka ba Kuma zai fiye maka sauki ka hakura da harkar.


Abu Na hudu, Karka debo kudi masu yawa sosae kace zaka zuba a wannan harkar musamman wanda zaka bukaci yin amfani dasu zuwa Dan wani lokaci kadan, sabida uncertainty na kasuwar wato 'rashin tabbas'


Abu Na Biyar, ba'a zuwa da kudi kadan ace za'ayi Investing a crypto, domin shiyasa ma Akace kayi binceke ka gano Coins masu ingancin inda zaka zuba kudinka, domin a mutanenmu ne zakaga wani yazo yana kokarin siyan coin na 2k Koh 1k  kaga wannan ai yaudarar Kai ne, wannan kudin Koh iya Network/Transaction fees ya cinyeta. da wanda zaiyi Investing da 1k Koh 2k a Crypto da Wanda ya Jefar da 1k Koh 2k din Yana sane dukka Daya kuke sabida kaje ka zuba a bitalmanin yahudawa gwandama da sadaka kayi wata kila ka Sami Lada, Amma bawai Hakan Kuma Yana nufin ka Debi abinda yafi karfinka ka zuba ba hakan shima gangancine, shiyasa akecewa 'invest what you can afford to loose' idan kaje ka ciyo bashin manya manyan Kudade ka zuba a crypto wannan Kuma you are on your own! idan ka sake saika shiga turu. 


Amma wasu suna fakewa da cewar ai su farin shigane shiyasa zasu Fara da kadan, toh wannan harkar ba Haka takeba, Shiyasa akace Do your Own research ma Before you get in. indai kasan Cewa bakada wani hope akan coin/token kaje ka siya,  toh wannan baka da bambanci da Dan caca.


a dinga saka kudi da lissafi.


Abu Na Shida, Dole Ka Zama Mai bincike sosai indai da gaske kakeson kayi harkar, domin ba kawai Investing akeyi a koma gefe ba. kodama ace trading kakeyi Dole ka Dinga bibiyar abubuwa domin Samun bayanai akan wasu abubuwan,  ciki Harda sababbi/tsofaffin Cryptos masu Muhimmanci da inganci, Da Kuma important news karsu dinga huce ka.


YADDA AKE BINCIKE AKAN COIN!


Da farko duk sanda kaga project ana tallansa Koh Kuma wani ya tura maka Contract address dinsa yace ka siya, Abinda zaka farayi shine ka Fara Neman group dinsa na Telegram ka shiga ciki, Bayan ka shiga saika bincika kaga Members nawane a wannan group din, Sannan Kuma saika kiyasta adadin Wadanda Suke online da Kuma total members na group din, hikimar hakan shine kagano cewar Real people ne a group din Koh Kuma may be sunyi amfani Da bot ne, wajen adding members din da babu su a zahiri?.


Mun sani cewar Akwai Fake members da ake siya, Kuma ayi amfani da bot wajen kawosu cikin group, wani group din zaka sameshi da misali 10k members Amma saikaga Kusan 9k a online toh kaga kanaji kasan Fake ne, Kuma yawanci zakaga Kusan Duk sanda ka duba adadin nasu bayayin kasa da haka kodayaushe 9k dinnan suna online., sabida an tsarasu ne su kasance online har abada saidai idan remove nasu akayi, toh kaga kanagani kasan karyace,  Babu wani group da Zai kasance Kamar haka. Koh Kuma kaga 10k members Sannan kaga basufi 200 a online ba, Suma kaga basa huce Haka saidai kasa da Haka toh shima kasan akwai matsala wadannan 200 din su kadaene real people a group din..


Menene yasa nayi magana akan wannan matsalar?

saboda Mugane cewar Duk token din da Muka sameshi da wannan matsalar toh tin daga Nan ma munsan Mai matsala ne, makaryatane A karshe zasu iya suyi Rugpull ne kawai tinda sun saka rashin gsky a tsarinsu.


Toh Bayan ka Gama yin wannan binciken, Sannan saika duba yanayin Members din community din, irin maganganun da sukeyi akan Project din, positive ne Koh kuwa negative. daga Nan saika Binciki Team din project din, who are they, Yaya kaga yanayinsu transparent ne wato ma'ana sun bayanna kansu Koh Kuma ba haka,  ba. bayyanawa Ina nufin Sun Dora picture a dp dinsu Koh kuwa Dukda shima akan iya Dora fake, Sannan ka duba Suna attending din mutane ta private Koh kuwa idan an tura musu message ma baya zuwa Koh Kuma basa kula mutane, Duk ta wadannan hanyoyin akan iya Gane rashin gaskiya da Kuma Rashin ingancin na Project tin anan.


WEBSITE


Bayan Duk ka Gama wadannan, Sannan saika dawo ka Nemi link na website dinsu ka kutsa Kai ciki, daka shiga saika karanta Duk wasu bayanai akansu, Kamar Road map dinsu da Irin su Token economics(Tokenomics) wato yanayin yadda ingancinsa yake da Kuma White paper dinsu Sannan Kuma da Jerin Developers dinsu a Kan website din idan sun Dora Sannan mu bincikensu mu tabbatar dai mutanene da basu boye kansu ba. Amma Fa musani Duk wadannan abubuwan Basu zasu tabbatar maka da cewar Wannan Project din Mai inganci bane, saikazo Maganar binciken Contract dinsa Sannan zaka iya tantance ingancinsa watakila.


 Toh Amma  Duk wadannan suna cikin abubuwan da zaka kasance ka tabbatar dasu Kafin Ka tafi next step domin Suma sunada matukar Muhimmanci.


CONTRACT


Sannan bayan ka Gama Duk wannan, baka Sami wata matsala ba, tou saika dawo cikin group din ka nemi su baka Contract address dinsa. ka tabbata Bakayi amfani da Contract address din da ka gani Yana yawo a postings din wasu mutane a media   ba, saboda a yanzu  kirkiran Token ba wani Abu bane Mai wahala,   idan aka kirkiri Token musamman idan akaga Mai ingancine sosai, scammers suna amfani da wannan damar su kirkiro same token irin wannan dauke da suna irin nasa, sabida idan sun Sami masu tsautsayi suje su siyi nasu maimakon Asalin na gaskiyar, Sai bayan watakila an gudu da kudinka Sannan kagane Real Project din watakila kazo kanayi musu complain cewar sun cuceka bayan Basu Suka cuceka ba wasu ne can daban.


abinda yasa na bayarda wannan shawarar shine Kasan wani Zai iya fadawa irin wannan tarkon, Sannan ya kawo Muku contract address, kaikuma idan bakayi wannan binciken ba Kaima zaka iya zuwa ka siya, toh a karshe shine zakaga dakai dashi Duk an fece da kudinku.


Toh shiyasa yakeda kyau bayan ka Gama wancan binceke kanason zaka siya, saika tambayesu a group dinsu cewar subaka address din, Kuma ka tabbata cewar admin ne Wanda ya turo maka address din.


toh bayan Duk ka huce wadannan, Dama already kasan A wanne Blockchain network Wannan token din yake, misali, Binance smartchain(BSC) ne ,ko  Ethereum Network(ERC), ko Tronchain da sauransu.  Toh saika Bude wannan Blockchain din Kamar misali idan BEP20 token ne wato(smartchain) sai ka Bude Bscscan. com  zakaga wani box da zaka iya searching token din, ta hanyar amfani da sunan token din Koh Kuma contract address dinsa. tou anan dolene kayi searching dinsa da Contract address bada suna ba domin akwai risk. domin anan ne zaka iya ganin fake tokens da aka kirkira da suna irin nashi, toh amma kaga cewar address shine Zai bambantasu. toh sai kayi paste din contrct address din da suka baka a group din anan saikayi searching zakaga sunansa ya fito saika tabashi Zai Bude maka.


Idan ya bude zakaga adadin holders dinshi, Sannan zaka iya kwantanta holders dinsa da mutanen daka Gani a telegram dinsu, wannan shima zai taimaka maka wajen samun wani bayanin.


bayan Haka saika duba kasa ka binciki yadda transactions dinsa yake kasancewa, Sannan ka duba Holders din kaga yanayinsu akwai whales da yawa a token din Koh kuwa, whales sune mutanen da suke masu manyan Kudade a ciki kaduba kaga wane wallet ce tafi kowacce mallakar wannan token daganan saika duba kagani wannan wallet din ta wane ce? Burnt address ne Koh Kuma SmartContract address ne wato address din dazamu ganshi da Dan wani Abu a farkonsa , wani symbol kamar memory Haka, toh Duk address din da Muka ganshi da irin wannan Kodai LP Tokens dinsune wato liquidity Koh Kuma wani SmartContract din daban, indai kaga wannan abin Mai Kamar memory a jikin contract address toh Koda ace Babu suna a jiki wannan ba wallet din normal holder bane, Amma wasu ma zamuga Da suna ajiki kamar wasu  zamuga an rubuta "pancakeswap" a jikinsu toh kaga wannan ya na nuna maka cewar Liquidity token ne wannan, a pancakeswap. 


Amma da zarar Kaga wata wallet wacce bamai wannan abun ba Kuma Tana rikeda High Percentage na Wannan token din Kamar kaga Tana rikeda 10% Koh 20% Koh 40% toh kaga wannan abun gudu ne.

Duk sanda kaga wallet Tana rikeda irin wannan kaso Koh kuma makamancinsa Bayan Kuma cewar ba'asan Mai wallet dinba ma'ana Kawai holder ne Wanda Babu Wanda Zai iya fadarsa toh wannan token din tin anan karka yarda ka siyeshi, wasu lokutan ma watakila Su team din Koh ince devs din sune Suke rikeda wannan wallet.


A takaice dai dakaga wata wallet da kaga baka yarda da ita ba Tana rikeda big percentage na Wannan token din toh karka siya kawai, idan Kuma kaje ka siya toh ka shiga caca Koh Kai Koh su.


Domin Ni bazan iya ce maka idan ka siya ba zakaci ribaba Koh Kuma idan ka siya zakaci riba, kawai dai Ina nuna maka cewar risk ne yin hakan.


domin kana iya siya kaci riba idan kanada rabo, Kafin suyiwa project din illa Kuma kana iya siya ka Rasa komai.


Sannan Bayan Duk kayi wannan saika Binciki Gundarin shi kanshi Contract din Duk a cikin wannan bscscan din, ka duba cewar project din ownership renounced ne Koh kuwa ma'ana Developers dinsa sunada ikon yin wani Abu akansa Kokuwa.


Yin wani Abu a kansa shine zasu iya Rage Masa yawane ta hanyar watakila Yi Masa Manual burn Koh Kuma zasu iya Kara Adadinsa shine ake cewa minting., ko Kuma dai wani Abu Mai kamada Haka, Duk Project din da za'a iya yin wadannan abubuwa akansa toh ka nutsu sosai wajen zuba kudinka a ciki.


Sannan Kuma ka bincika cewar sunada Developer's wallet ne Koh kuwa ? wato Owner's wallet kenan, idan da ita saika binciketa kaga How many percents na total supply  take holding, wato wanne adadi ne a cikin wannan wallet din tasu, wanne kaso ne, zasu iya cutar daku Investors idan Suka siyarda ita Koh kuwa abinda take rikeda shi bazai iya Yi Muku illa ba Koda an siyar. Koh Kuma  ma dai project din bashida Dev wallet wato sunyi Burning dinta already, Burning shine su tura tokens din a dead address shine zamudinga ganin (0x0000000000000000.....) wannan shine dead address, ana dura tokens cikinta ne saikaji ance anyi burning,  Wanda a zahiri ba burning akeyiba kawai an turasu inda baza'a Kara samin damar yin wani Abu a kansu ba har abada. 


Sannan ka duba sunada marketing wallet ne Koh Babu, marketing wallet itace wallet din da zasu dinga Amfani da ita wajen Tura Project din gaba wato wajen tallata shi kenan, ta hanyar Watakila Biyan influencers da sauran promoters a media su dinga tallatashi da Kuma yiwa holders giveaways da sauran Abubuwa irin yin contests Haka dukdai domin a taimaki Project din ya Shiga duniya mutane dayawa Suzo su zuba hannun jarinsu.


To yawancin Developers suna fakewa da wannan marketing wallet din suna Zaluntar Investors sai su nuna Muku cewar kawai ta marketing ce Amma a zahiri yankar wani adadi sukeyi a ciki suna siyarwa lokaci bayan lokaci shine zakaga token din kwata kwata Babu Wani Progress bayaci gaba, da anyi pumping dinsa sai su dumpershi, ku Kuma bakusan meyake faruwa ba. a Haka saisun Gama siyarda wallet dinnan tareda sauran holdings dinsu sannan a karshe watakila su gudu su barku da Project din a hannunku tinda sun Gama cin moriyarsa, toh kaga Duk Project din da bashida team kunga ai matacce ne Dole ya mutu murus domin Babu masu Gudanar dashi.


yanzu Haka akwai wani token Kusan abinda take Faruwa dashi kenan Wanda nasu baza'a Rasa masu shi ba anan, Amma bazan Fadi sunanshi ba sabida wasu dalilai.


LIQUIDITY


Toh kaga Duk wannan Yanadaga cikin abubuwan da zamu duba Sannan Kuma a karshe saimu binciki liquidity tokens din, anyi locking dinsu ne Koh kuwa a Bude Suke za'a iya ciresu a kowanne lokaci? domin munsan cewar liquidity yanada matukar Muhimmanci domin saida shine zaka iya samun damar siya Koh siyarda token , tou idan ya kasance an cireshi Kuma Kai a lokacin kana rikeda wannan token din kaga an Sami matsala kenan Dan bazaka iya siyarda naka ba. 


Shiyasa aka kawo dabarar yin locking dinsu domin Investors Sufi samun gamsuwar cewa baza'a iya cireshi ba bayan sun siya harsai lokacin dazai Bude yayi.


Amma fa musani bawai Locking dinsa anayine forever ba anayine for a specified time Kamar 2hrs,10hrs,1week,4weeks,3months 1yr,5yrs da sauransu ya danganta da yadda sukaga dama tou shiyasa yakeda kyau kanemi subaka link na inda sukayi locking dinsa kamar irin dexlock dinnan da sauran platforms saika shiga ka duba zuwa wanne lokaci akayi locking dinsa, kaga daganan saika yankewa kanka decision cewar ka siya Koh kuwa karka siya.


Shine ya Sanya wasu lokutan team indai sun tabbata masu gaskiyane sosai Suke burning din LP tokens din, yin burning shine su turasu zuwa (0x0000000000...) wato dead address kenan, idan Suka turasu cikin Nan bawai ana nufin an qona liquidity din bane kurmus, an turashi inda baza'a iya samun damar da za'a cireshi ne, har abada take nufi. Babu Wanda Zai iya cireshi domin sun turashi inda bazai dawo ba, sun Kona ticket din dazai Basu wannan damar.


Toh Amma fa musani cewar bawai sai anyi burning liquidity Sannan Project yakeda inganci ba, wasu Sunayin locking dinsa ne watakila sabida wasu dalilai , kamar misali suyi locking dinsa sabida sunasa Rai cewar zuwa Dan wani lokaci sunaso zasuyi migrating dinsu zuwa Kan wani platform din daban Koh Kuma wani exchange daban, Koh Kuma sunasa Rai cewar Nan gaba zasu kirkiri exchange dinsu ta kansu, toh sai suyi locking dinsa Kafin wannan exchange tasu tazo su mayardashi kanta. Koh Kuma Watakila  inda sukayi locking din nashi wataran na iya zama outdated ma'ana version din ya Zama old modern mutane sun daina amfani dashi sosai Koh kuma yadan sami wata matsala Koh Kuma An kawo wasu sababbin features Wadanda shi bashida su, toh Wannan shine Zai Basu damar idan an samu irin  wannan problems din suyi migrating dinsu su mayardasu sabon waje Mai kyau Domin komai yaci gaba da Tafiya daidai.


Toh Wannan dai kusan shine abubuwan da zamu Dan Lura dasu.


Allah yasa mudace. Ameeeeen ya Allah

Kayi share ga yan uwa da abokai 

FUKANMU NA SADA ZUMUNTA 
https://www.facebook.com/netage001/

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor