ABINCI DAKE KARAWA NAMIJI DA MACE SHA'AWA WURIN JIMA'I



ABINCI DAKE KARAWA NAMIJI SHA'AWA WURIN JIMA'I:



GARGADI: duk Wanda baya DA aure ya rage cin su kuma: domin yana tada sha'awa:


MA'AURATA IDAN KA TABBATAR ZAKAYI JIMA'I YAU ZAKA CI WANNAN ZAI TAIMAKA SOSAI.



1.Ridi


Ta yiwu ka yi mamakin am ambaci ridi, to ba abin mamaki game da haka don kuwa masana sun tabbatar da cewa yana kunshe da sanadarai na zinc da ke habaka yawan maniyyi ga namiji wanda hakan ke kara masa sha'awa.




2.Kankana

Wani bincike da aka gudanar a shekara ta 2008, ya nuna yadda kankana ke kara kuzari ga namiji, saboda wasu muhimman sanadaran da ta ke kunshe da su, harma wasu sukan misalta ta da irin magungunan jima'i da wasu ke sha.




3. Barkono/Yaji.

Wasu ba su san dangantakar gudanuwar jini a jikin dan-adam da jima'i ba. Yadda al'amarin yake yayin da sha'awar mutum ta motsa, hanyoyin jini da ke jikin al'aurarsa sukan bude sai jini ya kwarara, hakan ya ke sanya al'aurar ta sa yin karfi har ya samu damar gabatar da jima'i ba tare da matsala ba.




To shi barkono yana da sinadaran da suke aiwatar da irin wannan aiki a jikin dan-adam. Amma ba ana nufin mutum ya debi yaji ya sha ba, a'a zai hada shine da abinci. Haka nan kuma ana fadakar da mutane wajen takaita amfani da shi,musamman ga wadanda idan sun ci da yawa zai haifar musu da wata matsalar.

KARANTA:



4.Citta

Ita ma citta tana aiki ne kwatankwacin na yaji. Kamar yadda yaji ke taimakawa wajen kwararar jini zuwa ga al'aura namiji, haka ita ma ta ke yi. Sai dai kari akan na barkono ita tana kara lafiyar hanyoyin jinin.




5.Ya Yan kabewa

Ba shakka yayan kabewa na kunshe da sanadarai da ke kara sha'awa da kuma kuzari ga namiji.




6. Ayaba.

Masana sun gano cewa ita ayaba tana kunshe da sinadarin potassium, hakan ya sa masanan suka bayyana yadda ta ke karawa namiji kuzari, musamman idan ya ci mintuna 30 kafin saduwa da iyali.




7.Dankali

Dankali ko na gargajiya ko na turawa shima yana kunshe da sinadari potassium da ke inganta karfin mazakutar namiji, hakan kuma na inganta saduwa tsakanin ma'aurata.




8.Gyada

Ita kuwa gyada wani sinadari ta ke kunshe da shi da ake kiran sa amino acid L-arginine da turanci, shi wannan sinadari na taimakawa wajen dadewar gaban namiji a mike.




9.Tafarnuwa

Shekaru dubbai da suka shude mutanen kasar masar ke amfani da tafarnuwa don gudanar da magungunan matsalolin jiki dabam-dabam. Har ya zuwa wannan zamani da masana suka gudanar da bincike na zamani don tabbatar da irin alfanunta ga lafiyar dan-adam.




Binciken zamanin ya tabbatar da cewa ita tafarnuwa na gyara hanyoyin jini, kuma mun bayyana a sama yadda gudanuwar jini ke da alaka da mikewar gaban namiji. Hakanan tana gyara zuciya wadda itama an san aikinta na wajen tunkuda jini cikin jiki. Don haka wannan na bayuwa zuwa ga karfin al'aura yayin jima'i




10 Kwai

Ba sai an fada ba mun san kwai na kunshe da sinadarai masu gina jiki. Game da jima'i kuwa akwai sinadaran B6 da B5. Bincike ya nuna wadannan sinadarai suna kawar da damuwa, su kuma inganta sha'awa jima'i ga namiji.


0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor