ADDU’AR DA ZAKA YI WA AMARYA RANAR DA KA SHIGA DAKINTA


 ADDU’AR DA ZAKA YI WA AMARYA RANAR DA KA SHIGA DAKINTA.


Yana daga cikin hanyar samun zuriya tagari yin sallah ta nafila raka'a biyu, lokacin da Ka shiga xakin amarya a daren farko.


Sannan mutun ya xora hannunsa a kan matarsa, sai ya karanta addu'ar da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya koyar.


Addu’ar kuwa ita ce: ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻰ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺧَﻴْﺮَﻫَﺎ ﻭَﺧَﻴْﺮَ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦْ ﺷَﺮِّﻫَﺎ ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪ *Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alayhi.*


ADDU’AR SADUWA. (Sex )


Haka nan ma yin addu'a yayin jima'i domin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce duk wanda ya yi addu'a yayin

Jima'i, idan Allah ya qaddara samun xa a lokacin saduwar

(Jima’i), shaixan ba zai cutar/

shafe shi ba da iznin Allah. 


Ga addu’ar kamar haka: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺟﻨﺒﻨﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ، ﻭﺟﻨﺐ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﺘﻨﺎ 


BismilLahi Allahumma jannibina Shayxana wajannibi Shayxana ma

razaqatana.


KARANTA:

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor