AMFANIN SHAN RUWA DA SAFE KAFIN ACI KOMAI


AMFANIN SHAN RUWA DA SAFE KAFIN ACI KOMAI:

1. Yana tsaftace hanji:

Shan ruwa da safe yana taimakawa wajen tsaftace haji. Yana taimakawa wajen sanyawa hanji ya motsa inda hakan zai sanya sauran abinda ke cikin narkewa. Masana sun shawarci cewa idan mutum ya fuskanci matsala ta cunkushewar ciki, ya sha ruwa da yawa, domin yana taimakawa wajen wanke hanji, ya kuma sanya halittun cikin mutum daidaituwa.

Masana sun bayyana cewa shan ruwa da safe kafin mutum ya ci komai yana taimakawa wajen wanke hanji, da kuma narkar da sauran abinda ya rage a ciki.


2. Yana taimakawa wajen fitar da abubuwa masu illa a jiki :

Shan ruwa da safe kafin a ci komai na taimakawa wajen fitar da duk wasu abubuwa masu illa daga jiki. Yana kawar da dukkan kwayoyin halitta masu illa daga jiki ya kuma tsaftace jiki. Fitar da wadannan kyayoyin halitta masu illa yana taimakawa wajen sanya fatar jikin mutum tayi kyau ya kuma sanya fuskar mutum ta dinga kyalli.

A jikin mutum akwai wasu kyayoyin halitta masu illa, shan ruwa da safe kafin a ci komai na taimakawa wajen wanke wadannan kwayoyin halitta.


3. Yanaa hana ciwon kai:

Babban dalilin da yake kawo ciwon kai shine rashin shan ruwa da yawa. Kishin ruwa yana sanya mutum ya dinga jin ciwon kai. Shan ruwa ba wai yana maganin ciwon kai bane kawai, yana taimakawa wajen hana warin jiki da warin baki da sauran wasu cututtuka.

Shan ruwa da safe na taimakawa wajen hana ciwon kai, warin jiki da kuma warin baki.

KARANTA:



4. Yana kawo yunwa:

Shan ruwa da safe kafin a ci abinci yana taimakawa wajen wanke ciki, inda hakan zai sanya mutum yaji yunwa.


5. Yana kara kuzari:

Shan ruwa da safe kafin a ci abinci yana taimakawa wajen sanya kwayoyin halittar mutum su samu kuzari, inda hakan zai sanya jikin mutum ya samu kuzari.


6. Yana sanya saurin girma:

Mutumin da yake rage kiba ya dingaa shan ruwa mai yawa saboda yana taimakawa matuka. Shan ruwa da safe yana taimakawa wajen kara girma da kashi 25 cikin dari. Haka kuma saurin narkewar abinci yana taimakawa wajen rage kiba sosai.


7. Yana taimakawa wajen rage kiba:

Ruwa bashi da sinadarin kara kiba, hakan ya sanya shan ruwa musamman da safe kafin a ci abinci yake taimakawa wajeen rage kiba, haka kuma yana taimakawa wajen wanke cututtukan dake ciki da kuma hana kumburin ciki. Yayin da ruwa yake sanya kuzari, haka kuma yana taimakawa wajen kone mai. Shan ruwa da yawa yana daya daga cikin manyan hanyoyi na rage kiba.

Shan ruwa da yawa yana taimakawa matuka wajen rage kiba da kuma hana kumburin ciki.

8. Yana gyara fata:

Kishin ruwa na daya cikin matsalolin dake kawo matsalar fata. Rashin shan ruwa yana sanya fata ta dinga nadewa. Shan ruwa da safe kafin a ci abinci yana taimakawa jini gudana a jikin mutum, hakan yana taimakawa wajen gyara fatar mutum. Haka kuma yana taimakawa wajen kashe kwayoyin cuta dake jikin fata, ya kuma sanya fatar mutum ta kara haske.


Shan ruwa da safe na taimakawa wajen gyara fatar mutum da kuma sanya fatar mutum ta dinga kyalli.

9. Yana gyara gashi:

Yawan shan ruwa da safe yana taimakawa wajen fitar gashi da kuma sanya gashi yayi kyalli. Ruwa yana dauke da kaso 1 cikin 4 na sinadaran dake samar da gashi, saboda haka rashin shan isasshen ruwa yakan sanya gashin mutum ya ki fita yadda ya kamata ya kuma samu rauni. Shan ruwa da yawa yana taimakawa wajen tsirar gashi da kuma kara lafiyar gashi.

Shan ruwa da yawa yana taimakawa matuka wajen tsirar gashi da kuma gyara gashi, haka kuma rashin shan ruwa yana sanya gashin mutum yaki fita ya kuma dinga lalacewa.


10. Yana maganin ciwon koda:

Shan ruwa da safe kafin mutum ya ci abinci yana taimakawa wajen hana kamuwa da ciwon koda. Haka kuma yana hana kamuwa da cutar mafitsara. Ruwa yana juya sinadarin ruwan dake cikin koda ya dinga wanke ta.




11. Yana karfafa tsarin jiki:

Shan ruwa yana taimakawa wajen wanke kwayoyin cututtuka ya kuma hana cuta yaduwa a jikin mutum. Wannan yana taimakawa matuka wajen daidaita tsarin halittar mutum sannan kuma ya hana jiki daga kamuwa da cuta.

Shan ruwa kofi daya a kullum da safe yana taimakawa jikin mutum ya sami duka wadannan muhimman abubuwa.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor