ANGO YA SAKI AMARYARSA A DAREN FARKO


ƘAWAYE SUN SA ANGO YA SAKI AMARYARSA A DAREN FARKO


Wani Ango ne dai ya saki Amaryarsa saki É—aya a Daren da aka kawota tun kafin ya shiga ÆŠakin.


Hakan dai ya biyo bayan da Æ™awayen Amaryar ne suka kulle Æ™ofa suka ce sam bazasu buÉ—e Æ™ofar ÆŠakin ba sai an biyasu kuÉ—in Al'ada ta sayen Baki har Naira Dubu ÆŠari Biyu (₦200,000) wuri na gugar wuri.


Da jin haka sai Abokan Ango suka yi ta luguden laÉ“É“a da Æ™awayen Amaryar don neman ayi musu sassauci. Bayan da Angon yaga abin ya Æ™i ci kuma ya Æ™i cinyewa ga dare na Æ™ara tsawo anara É“ata lokaci tunda Ƙawayen sun kafe kan sai an biya ₦200,000 yaga dai dagaske sukeyi, sai yace a basu Naira Dubu Talatin (₦30,000).


Bayan an Æ™idayo Dubu Talatin aka ce gashi su buÉ—e Ƙofar sai kawai Æ™awayen Amaryar suka Æ™eÆ™asa Æ™asa suka ce basu yarda ba, Naira Dubu Talatin (₦30,000) tayi kaÉ—an. Don haka ba zasu bude kofar ba sai an Ƙaro.


Daga nan sai Angon ya kira Amaryarsa a waya sau biyu, ita kuma taƙi ɗaga wayar Angonta.


Abinka da ƙaddara, aikuwa cikin fushi sai Angon ya ɗauki wayarsa ya turawa Amaryarsa saƙon karta-kwana wato (Text Message), cewa, 'Na saketa saki ɗaya.'


Kafin kace kwabo! Ƙawayen sun buɗe Ƙofar kowa ta gudu gidansu suka bar Amarya da Sallallami cikin baƙin ciki.


Iyaye da Al'umma sai a É—auki darasi!

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor