TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

 


TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Yayin da Annabi ﷺ ya cika Shekara biyu a hannun Halima (RA), sai ta mayar dashi wajen Mahaifiyarsa. A wannan lokaci, sai kuma ta tsinci kanta tana mai bakin ciki, zuciyarta tana kuna, kuma idanuwanta suna zubar da hawaye saboda bata son rabuwa dashi.

Don haka sai ta sake neman alfarma wajen mahaifiyar tasa Amina (AS) da ta lamunce mata ta kara kasancewa tare dashi zuwa wani dan lokaci. Kuma ta yi sa'a, Sayyidatuna Amina (AS) mai yawan karamci da alfarma ce, don haka sai ta amince mata. Cikin farin ciki sai Halima (RA) ta dauke shi ﷺ ta koma dashi.

A wannan lokaci na rayuwarsa tare da Halima (RA) da iyalanta, Annabi ﷺ ya kasance tare da 'ya'yanta yake yin komai cikin farin ciki, kuma tare suke fita kiwon tumaki zuwa cikin dajin bayan kauyen. Wasu lokutan kuma, Halima (RA) takan ganshi ya zauna shi kadai.

A halin wannan tafiya kiwon ne, wata rana, sai Allah Ya aiko wasu mala'iku guda biyu suka zo wajen Annabi ﷺ suka kama shi suka kwantar dashi, suka tsaga kirjinsa suka fitar da zuciyarsa suka wanketa da wani ruwa cikin wata tasa, kuma suka mayar da zuciyar da izinin Allah. Ta haka ne, Allah Madaukaki Ya wanke masa zuciyarsa ta zama tsarkakakkiya, saboda Allah Yana so ne ya zamo mafi tsarki daga dukkan wani mutum a duniya, domin shine cikamakin Annabawa.

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

ﺃَﻟَﻢْ ﻧَﺸْﺮَﺡْ ﻟَﻚَ ﺻَﺪْﺭَﻙ * ﻭَﻭَﺿَﻌْﻨَﺎ ﻋَﻨْﻚَ ﻭِﺯْﺭَﻙ * ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺃَﻧْﻘَﺾَ ﻇَﻬْﺮَﻙَ * ﻭَﺭَﻓَﻌْﻨَﺎ ﻟَﻚَ ﺫِﻛْﺮَﻙ * ﻓَﺈِﻥَّ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮِ ﻳُﺴْﺮًﺍ * ﺇِﻥَّ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮِ ﻳُﺴْﺮًﺍ * ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻓَﺮَﻏْﺖَ ﻓَﺎﻧْﺼَﺐْ * ﻭَﺇِﻟَﻰٰ ﺭَﺑِّﻚَ ﻓَﺎﺭْﻏَﺐْ

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai:

"Ashe, Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)? Kuma Kuma Muka dauke maka nauyinka, Wanda ya nauyayi bãyanka? Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka? To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah). Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi!" (Suratul Sharhi: 94 :1-8)

Sauran yaran da Annabi ﷺ yake tare dasu a wajen kiwon sun ga lokacin da mala'ikun nan a sifar mutane suka kama shi suka kwantar dashi suka tsaga kirjinsa, don haka sai suka tsorata, kuma suka garzaya a guje domin sanar da Halima (RA) abinda ke faruwa.

Ai kuwa koda ta ji haka sai ta yo lullu6i a tsorace ta fito tare da wasu mutane da suka yo mata rakiya domin ta ga halin da Annabi ﷺ yake ciki. Amma ga mamakinta, sai ta tarar dashi zaune a wajen dabbobin babu alamun wani abu ma ya same shi, ta tambaye shi me ya same shi? Ya gaya mata cewa babu abinda ya same shi.

Duk da haka dai, hankalin Halima (RA) bai samu nutsuwa ba, don haka ta yanke shawarar ta mayar dashi wajen mahaifiyarsa kar wani mummunan abu ya same shi. In kuwa har wata cuta ta same shi, to da wacce fuska za ta je wa mahaifiyarsa? Don haka sai ta ayyana cewa yanzu ya zama dole ta hakura ta mayarwa mahaifiyarsa yaronta. Kuma hakan aka yi, ta dauke shi ﷺ ta dawo dashi wajen mahaifiyarshi.

Lokacin da Halima (RA) ta mayar dashi wajen mahaifiyarsa Sayyidatuna Amina (AS), mahaifiyar tasa ta yaba kwarai da irin tattalin da Halima ta yi masa, ta ganshi ya zama yaro mai cikakken koshin lafiya da karfin jiki.

Wannan rayuwa da Annabi ﷺ yayi a wajen Halima dai, ba zai manta da ita ba. Kuma har girmansa bai ta6a mantawa da lokacin farin ciki da yayi rayuwa da Halima 'yar Banu Sa'ad ba, kuma har numfashinsa na karshe, ya kasance yana alakanta kansa da Banu Sa'ad.

Annabi Muhammadu ﷺ ya dawo karkashin kulawar mahaifiyarsa a garin Makkah ne lokacin da yana kusan shekara uku da haihuwa. Bayan wasu shekara ukun (shida kenan), sai Sayyidatuna Amina (AS) ta kudurci aniyyar kai shi ziyarar kawunnansa dake Yathrib (Madina). Sai ta gaya wa kuyangarta Barakah cewa tare da ita zasu tafi, don haka ta shirya masu duk abubuwan da zasu bukata a yayin wannan doguwar tafiya, daga nan sai suka shiga wani ayarin fatake mai tafiya zuwa can.

Sun zauna a Yathrib na kusan wata guda, kuma Annabi ﷺ ya ji dadin wannan ziyara, yayin da ya kasance tare da 'yan uwansa ('ya'yan kawunnansa).

A kan hanyarsu ta dawowa zuwa Makkah ne, sai Sayyidatuna Amina (AS) ta kamu da rashin lafiya, ashe kuma ajali ne ya zo mata, sai ta rasu a kan hanya Aka binneta a wani kauye wanda ake kira "ABWA" wanda ba ya da nisa daga Yathrib/Madina.

Annabi ﷺ ya dawo Makkah cikin bakin ciki marar misaltuwa, tare da kuyangar mahaifiyarsa. Yanzu duka-duka shekarunsa shida a duniya, amma gashi ya rasa duka mahaifansa.

Daga nan sai Kakansa Abdul-Muddalib ya kar6i renonsa ﷺ , kuma ya ci gaba da nuna masa tsantsar soyayya, a koda yaushe yana kusa dashi, kuma duk inda zai je yana tafiya ne tare dashi.

Yana daga al'adar Abdul-Muddalib, yakan zauna akan buzu a kusa da dakin Ka'abah, inda a ko yaushe baka rasa mutane kewaye dashi wadanda ke zuwa magana dashi, amma babu wanda yake bai wa damar zama akan wannan buzun, sai jikansa Annabi Muhammadu ﷺ kadai. Wannan yana nuna irin kusancin da yake dashi a wajensa.

Lokuta da yawa, an sha jin Abdul-Muddalib yana cewa, "Tabbas, wannan yaron zai zama wani muhimmin mutum wata rana!"

Allah Yayi dadin tsira da Aminchi a bisa Annabi Muhammadu da Alayensa da Mahaifansa da Kakanninsa baki daya, Allah Ya bamu albarkacin dukkan danginsa da masoyansa, Amin.


Ayi Share Domin Amfanar Yan Uwa.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor