Zainab ta zama jami'ar hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA
Zainab Aliyu kenan da Hukumomin 'Kasar Saudiyya suka kama Cikin kuskure a shekarar 2018 bayan wasu gur'batattun Ma'aikatan filin Jirgin sama suka saka Mata haramtattun Kwayoyi a Cikin jakar ta.
Cikin Ikon Allah, yau ga Zainab ta zama ma'aikaciyar Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Najeriya ta NDLEA
An sako Zainab ne daga kurkukun Saudiyya a ranar 30 ga watan Afrilun 2019 bayan an gano cewa ba ta da laifi wasu ne suka yi mata sharri.
A yanzu matashiyar, mai shekara 25, ta kammala karɓar horo a Kwalejin horas da jami'an hukumar ta NDLEA da ke Katon Rikkos a jihar Filato da ke Najeriya.
Bayan kammala karɓar horon, ta fito da anini ɗaya a matsayin 'Assistant Superintendent of Narcotics'.
Post a Comment