AMFANIN AYABA A JIKIN DAN ADAM:
Ayaba na daga cikin ya yan itatuwa da mutane suke yawan amfani da ita sosai a duniya ba tareda sun san amfanin ta ba.
Ayaba na dauke da sinadaran nutrients kamar haka :
- Potassium
- Magnesium
- Vitamin B and C
- Copper
- Manganese
- Carbs
- Fiber
Ga kadan daga cikin amfanin Ayaba a jikin dan Adam:
1- Yana taimaka ga masu niyar daina shan sigari.
2- Yana Karawa kwakwalwa kaifi.
3- Yana saukake ciwon Al'ada.
4- Yana kare mutun daga karancin jini.
5- Yana kare mutum daga kamuwa da cutar zuciya.
6- Yana kara karfin kashi.
7- Ayaba na kare mutum daga kamuwa da cutar hawan jini sannan kuma yana samar da sauki wa mutanen dake fama da cutar.
8- Yana hana bacewan ciki(zawo).
9- Yana taimaka ga masu ciwon ulcer.
10- Yana taimaka wajen samun saukin bahaya.
11- Yana taimaka wajen rage kiba.
12- Yana gyera fatan mutum (skin)
Ko kusan Ayabar da ta nuna tafara baki tana da amfani ga lafiyar dan Adam ?
1- Tana aiki a matsayin Antacids ( magungunan ulcer na ruwa irin su mist magnesium ) tana taimaka wajen saukake ciwon zuciya na gyenbon ciki.
2- Wajen da yayi baki baki tana dauke da sinadarai wanda suke yaki da ko wacce irin cancer wanda ake kiransu ( Tumor Necrosis Factor).
3- Tana dauke da sinadaran fiber wanda yake taimaka wajen daidaita cholesterol na jikin mutum , hakan yasa masana kimiya sukace tana kare ko wacce irin cuta na zuciya.
4- Tana dauke da sinadaran wanke ciki ko kuma ince sinadirai masu kare jiki daga abincin da kaci yazame maka guba da kuma wassu cututtuka (Antioxidant) hakan tasa masana kimiya sukace tana karawa sinadaran garkuwan jiki (Immunity) Karfi.
5- Yana kare jikin dan Adam daga samun matsalar rashin narkewan abinci (Indigestion).
6- Daga karshe yana karawa kwakwalwar dan Adam (Brain) kaifi.
Allah Ya Kara mana lafiya.
Don Allah kuyi sharing group group
Post a Comment