Video: Boko haram sun harbo roket cikin birnin Maiduguri

 

Bayanai daga Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu da ake kyautata zaton mayakan ISWAP ne sun harba rokoki zuwa wasu sassan garin Maiduguri da suka hada da unguwannin Gomari Airport da kuma 1000 Housing Estate, lamarin da yayi sanadin rushewar wasu gine gine.

Sai dai Kawo yanzu babu rahoton samun hasarar rai, a yayinda jirgin sojin Najeriye ke shawagi domin tabbatar da tsaro, kamar yadda wakilin sashin Hausa na RFI a garin na Maiduguri ya tabbatar

Har ila yau wani makamin roka ya sauka a Gomari yankin dake da nisan kilomita akalla 4 daga filin jiragen sama na Maidugurin, babban birnin jihar Borno

Wata majiyar soji ta bayyana cewa, dakarun Najeriya. sun yi amfani da manyan makamai wajen bude wuta kan mayakan na ISWAP da suka tsinkaya a wajen  Maiduguri, inda suka shafe tsawon lokaci suna artabu.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor