An soma nuna tsiraici acikin shirin Shakundum

 


Masu Shirya Film din Hausa sun fara saka batsa acikin Fina-finai masu dogon Zango

Dan jarida mai bincike kan fina-finan hausa kana mai fashin baki akan harkar fina finai Yusuf Abacha, ya gano wasu fina-finan Hausa guda goma Top 10 wadanda saka nuno batsa aciki daga cikin guda 10 ya duba daya.


Akwai wani Film mai suna Shakundum kamfanin shirya fina-finan Hausa Sultan Film Factory suka tsara su ka Shirya a cikin film Esposid 10 a daidai mintuna 20: dakiƙa 29 an nuno jarumin wasan barkwanci Yamu Baba wanda aka fi sani Da mijin Sambisa an nuna yana cire wandonsa.


Wannan abun ya sabawa ƙa'idojin Addinai hakan sam bai dace ba, yara da mata suna kallon fina-finan Hausa masu dogon zango musamman ma a wannan lokacinda, ake yayin fina-finai masu dogon zango.


Wannan bashine karo farƙo da ɗan jarida Yusuf Abacha, yana bankado irin wadanan matsalolin ba, a watan December 2021 Yusuf Abacha ya gano yadda Naziru sarkin waka ya aibatnta aikin jarida a cikin film din labarina.


Yusuf Abacha ya lissafa fina-finai guda goma Da suka nuna batsa a zahiri.

KARANTA:

Menene Film Kuma ya take da Rayuwar Yara da mata a yanzu ?


'Yan Fim, wadanda aka fi sani da 'Yan Drama, suna daga cikin rassa na Kungiyoyin Boko Aqida mafi hatsari ga al'umma, kuma mafi saurin tasiri a kanta, saboda su ne suke yada barnarsu a aikace, kuma a cikin jama'a ba tare da wani tsaiko ko tsangwama ba.


Duka kungiyoyin Boko Aqida kusan sun yi tarayya a kan halasta Alfasha da yaki da Addinai da kyawawan dabi'u, inda dukkansu sun dauki wannan a matsayin babbar manufa, kuma babban jigo a tafiyar tasu.


Kungiyoyin Boko Aqida, tun daga kan Masuniya (Freemasonry, Masonic), da Sakulanci (Secularism), da Gurguzanci (Socialism), da Kwaminisanci (Communism), Ilhadi (Atheism), duka wadannan kungiyoyi da hanyoyi na tsarin rayuwa, dukkansu sun yi tarayya wajen jefar da Addini a cikin rayuwa, da kuma jefar da kyawawan halaye da dabi'u, bisa ikirarin 'yancin rayuwa.


To su wadannan 'Yan Fim, an samar da su ne don yada Aqidar 'yancin rayuwa ba tare da zama karkashin qaidin Addini ko kyawawan dabi'u na kunya da kamun kai ba, tare da yaki da su. Shi ya sa za a ga fina – finai da ake yi duka kusan suna kira ne ga bayyana tsiraici da yaduwar alfasha a cikin al'umma ta hanyar cire shamaki tsakanin jinsin maza da mata.


Shi ya sa 'Yan Fim suka zama hanya mafi muhimmanci ga Kungiyoyin Boko Aqida wajen watsa barna da sharrinsu a cikin al'umma.


A Turai, akwai kungiya ta Boko Aqida da ta yi fice da wannar manufa ta halasta alfasha da rushe kyawawan halaye (Libertine), wacce ake kira da 'Yan wayewa (Modernity), wadanda suka tattaro tunaninsu da Aqidunsu daga wasu munanan kungiyoyi masu yawa, kamar Marxism, Existentialism, Freudian, Darwinism, Surrealism, Avatar.


Saboda haka, wannar Aqida da wannar hanya, kamar yadda ta fi muni a Turai, haka ita ce Aqida mafi muni cikin masu dangantuwa zuwa ga Muslunci.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor