Wannan mutumumin ya yanke azzakarinsa da kansa

 


Mutumin da ya datse al’aurarsa “domin kawar da sha’awar jima’i a Benuwe, yace zai mayar da hankali kan bautar Allah


Terhemen Anongo, mai shekaru 44 da haihuwa mazaunin Gboko a jihar Benue, ya cire al’aurarsa “domin kawar da sha’awar jima’i”.


Anongo, wanda ya yi murabus a makarantar likitanci, ya yi ikirarin matakin zai ba shi damar bauta wa Allah yadda ya kamata.


A shekarar da ta gabata, ya cire daya daga cikin ’ya’yan marainan sa da kansa, inda ya kusa rasa ransa a cikin wannan aikin.


Ya fara fitowa fili ne a cikin watan Maris bayan anyi masa tiyata, wanda ya yi sanadin zubar da jini.

KARANTA:

Shigowar wadanda suka san halin da yake ciki a kan lokaci ya ceto lamarin yayin da likitocin suka yi ta zagayawa domin ba shi kulawa.


Anongo, wanda ya bar makarantar koyon aikin likitanci ta Jami’ar Ibadan bisa zargin rashin lafiya, ya ce ya yi hakan ne bisa imaninsa na addini cewa tun da bai yi aure ba, yana bukatar ya bauta wa Allah da aminci.


"Ina lafiya. Babu matsala, ina jira kawai lokacin da raunin zai warke don in cire dinkin. " Inji shi

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor