JINNUL ASHIQ (ALJANIN SOYAYYA)


 JINNUL ASHIQ (ALJANIN SOYAYYA)


MENE NE JINNUL ASHIQ?


Pls Read and share to Others group,friends and contact as Sadakatul Jariyyah


- JINNUL ASHIQ Wani irin aljani ne wanda yake

shiga Jikin Mata saboda tsananin soyayyar da

yake musu.


MENENE DALILAN SHIGARSA:


Ayawancin lokuta yakan shiga ne ta dalilin

SOYAYYA. amma awasu lokutan yakan shiga ta

wasu dalilan sannan daga baya ya juye ya zama

na soyayya din.


WACCE IRIN CUTARWA YAKE YI??


Daga cikin nau'in cutarwar da yake yiwa 'Yan-

Mata akwai:


1. Yakan Kore musu samari.


 komai soyayyar da

saurayi yake ma budurwa, sai ita kuma taji ta tsaneshi. koda kuwa ita ce ta fara furta masa

soyayyar.


2. Yakan sanya ma budurwa Bakin-Jini mai tsanani. ko kuma ya hana su samarin zuwa wajenta. Ko da sun furta suna Qaunarta, amma babu damar suzo wajenta zance.


3. Yakan rika zuwa yana saduwa da yarinya. zata

rika ganinsa yana zuwa mata amafarki yana saduwa da ita. Acikin Siffar Saurayinta ko mahaifinta, ko yayanta, ko kuma wani mutum wanda ta sani ko kuma wanda ma bata sani ba.


4. Motsawar jinyoyi kala-kala da zarar anyi mata maganar aure. sai kaga ta kama zlciwon kai da zazzabi ba dare ba rana.


5. Daukewar Sha'awa. yarinya zata rinka ji acikin ranta cewar ita fa bata son aure. kuma zataji bata bukatar duk wani Namiji.


6. Wata ma idan abun ya fara nisa, ko unguwa zata je, sai ta rika jin kamar wani yana tafiya

abayanta.. To Aljanin ne yake rakata.. Kuma yana bibbiyar mazajen da suke kallonta awaje. da zarar wani ya furta yana sonta, to Aljanin zai

shiga zuciyarsa ya sanya masa waswasi. har ya

shiriritar da shi.


7. Akwai wacce idan abun yayi nisa Aljanin zai rika zuwa mata AFILI QARARA yana saduwa da ita. koda da rana ne.


8. Akwai wacce aljanin zai rika sanya mata saurin Fushi tana fada da samari. da zarar sun fara soyayya da mutum sai taji Duk duniya bata

da Makiyi kamarsa.


9. Akwai wacce Aljaninta Har WARNING yake yiwa samari. zai kira mutum ta waya. yace masa Kar ya Qara ganinsa tare da wance.


TA YAYA ZAN GANE INA DASHI??


- Bayan wadannan alamomin da na lissafa, zai hada miki da yawan ciwon kai, faduwar gaba, Wasa da sallah, Qin karatun Alkur'ani, Taurin kai, rikicewar tunani, rashin barci, kasala, Rikicin jinin Al'ada, Saurin fushi, Mantuwar

karatu, da sauransu..


NAN GABA insha Allahu zamu fadi irin illolin da yake yiwa matan Aure. Da fatan Allah shi karemu. marassa lafiya kuma, Ya Allah ka basu lafiya ameeen.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor